Daga Awwal Umar Kontagora
Jam'iyyar National Democratic Coalition (NDC) reshen Jihar Neja ta bayyana cewa ta zaɓi Hon. Abdulrahman Awal a matsayin ɗan takararta na kujerar Majalisar Wakilai ta Tarayya mai wakiltar mazaɓar Bida, Gbako da Katcha ne bisa cancanta da irin gudummawar da yake bayarwa ga al'umma.
Sakataren jam'iyyar a jihar, Dr. Joseph Mamman, ne ya bayyana hakan yayin da yake sanya hannu kan takardar tabbatar da takarar Hon. Abdulrahman Awal domin zaɓen shekarar 2027.
Dr. Joseph ya ce jam'iyyar ta yi nazari mai zurfi bayan mutane da dama sun nuna sha'awar neman takarar, amma daga ƙarshe ta yanke shawarar bai wa Abdulrahman Awal tikitin takara saboda cancantarsa da kuma irin rawar da ya taka wajen ci gaban al'umma.
Ya bayyana cewa tsarin dimokuraɗiyya ya bai wa kowane ɗan ƙasa damar ba da gudummawarsa wajen ci gaban ƙasa, ba tare da la'akari da halin da yake ciki ba.
A cewarsa, duk da ƙalubalen da Hon. Abdulrahman Awal ke fuskanta a matsayinsa na mai buƙata ta musamman, hakan bai hana shi taka rawar gani a fannoni daban-daban na shugabanci da hidimtawa al'umma ba.
Ya kuma bayyana ƙwarin gwiwarsa cewa al'ummar ƙananan hukumomin Bida, Gbako da Katcha za su yi zaɓi bisa nagarta da cancanta.
Shi ma jigo a siyasar Kwankwasiyya a Jihar Neja kuma tsohon ɗan takarar kujerar Majalisar Dattawa, Hon. Danladi Umar Abdulhamid, ya bayyana Hon. Abdulrahman Awal a matsayin ɗan takarar da ya fi sauran 'yan takara cancanta.
Ya ce nakasar da yake da ita ba ta hana shi yin ayyukan ci gaban al'umma ba, inda ya ƙara da cewa ya yi abubuwan da wasu 'yan siyasa masu cikakkiyar lafiya ba su samu damar yi ba.
Hon. Danladi ya yi kira ga al'ummar Bida, Gbako da Katcha da su mara wa Abdulrahman baya, yana mai bayyana cewa yana da jajircewa da hangen nesa da za su amfani mazaɓar.
Da yake amsa tambayoyin manema labarai, Hon. Abdulrahman Awal ya ce takararsa ba ta kuɗi ba ce, kuma bai amince ya tsaya takara ba sai bayan ya tuntubi al'ummar mazaɓarsa.
"Ba mu da kuɗi, amma muna da Allah, kuma muna da ƙuri'un al'ummarmu. Duk mai son sanin ko wanene Abdulrahman Awal ya binciki tarihina da irin muƙaman da na riƙa da kuma ayyukan da na gudanar wajen yi wa al'umma hidima," in ji shi.
Ya ƙara da cewa a matsayinsa na ɗan asalin yankin kuma jinin sarauta, ya san irin buƙatun al'ummar mazaɓarsa, yana mai alƙawarin samar da wakilci nagari idan aka ba shi dama.
Hon. Abdulrahman Awal ya taɓa zama wakilin masu buƙata ta musamman na tsohuwar jam'iyyar NNPP a matakin ƙasa. Kafin haka kuma, ya taka rawa a harkokin siyasa tun daga jam'iyyar APC, inda ya shiga yakin neman zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Umar Mohammed Bago.
Ya bayyana cewa rashin bai wa masu buƙata ta musamman damar da ta dace a gwamnati da kuma rashin kula da wasu buƙatun al'umma ne suka sa ya sauya sheƙa zuwa NNPP a wancan lokaci, kafin daga bisani ya koma jam'iyyar NDC domin ci gaba da fafutukar siyasa.
Post a Comment