An Ƙaddamar Da Shirin Haɗin Gwiwar Hakar Ma'adinai Tsakanin Gwamnatin Neja Da Ƙungiyar NUMW A Zumba

Daga Awwal Umar Kontagora

Gwamnatin Jihar Neja ta ƙaddamar da shirin haɗin gwiwa da Ƙungiyar Ma'aikatan Hakar Ma'adinai ta Najeriya (Nigeria Union of Mine Workers – NUMW) domin inganta harkar haƙar ma'adinai tare da daƙile haƙar ma'adinai ba bisa ƙa'ida ba.

An ƙaddamar da shirin ne a sabon wurin haƙar ma'adinai mallakin gwamnatin jihar da ke ƙauyen Jan-Kasa, cikin gundumar Zumba ta Ƙaramar Hukumar Shiroro.

Da yake jawabi a wajen ƙaddamar da shirin, Daraktan Kula da Albarkatun Ƙasa na Jihar Neja, Mista Kolo Israel, ya bayyana cewa shiga kai tsaye da gwamnatin jihar ta yi cikin harkar haƙar ma'adinai na da nufin ƙarfafa tsarin gudanar da aikin da kuma kawo ƙarshen haƙar ma'adinai ba bisa ƙa'ida ba.

Ya ce sabon wurin aikin na ƙarƙashin kulawar kamfanin Zuma, mallakin gwamnatin jihar, kuma za a gudanar da aikin ne bisa haɗin gwiwa da Ƙungiyar NUMW, ta yadda za a raba ribar abin da aka haƙo tsakanin gwamnati, masu aikin haƙar ma'adinai da kuma ƙungiyar da ke kula da haƙƙoƙin ma'aikata.

Mista Kolo ya ƙara da cewa gwamnatin jihar za ta samar da ingantaccen tsaro a wurin aikin tare da tabbatar da bin duk sharuɗɗan yarjejeniyar da aka cimma tsakanin gwamnati da ƙungiyar.

A nasa jawabin, Shugaban Ƙungiyar NUMW, Kwamared Musa Adamu Nasko, ya bayyana cewa shigar gwamnatin cikin harkar haƙar ma'adinai zai ba ma'aikatan kariya daga matsalolin da suke fuskanta, musamman matsin lambar jami'an tsaro da kuma matsalar haƙar ma'adinai ba bisa doka ba.

Ya ce ƙungiyar na maraba da wannan tsari, domin zai amfani dukkan ɓangarorin da abin ya shafa. Ya kuma tabbatar da cewa ƙungiyar za ta gudanar da aikinta cikin gaskiya da riƙon amana, ba tare da kauce wa dokokin gwamnati da na ƙungiyar ba.

Shi ma Shugaban Kamfanin da zai jagoranci gudanar da aikin, Mista Shaba Maigida, ya bayyana cikakken goyon bayansa ga shirin, yana mai cewa zai gudanar da aikin bisa tsarin da gwamnati da NUMW suka amince da shi.

Ya ce ya shafe sama da shekaru 20 yana harkar haƙar ma'adinai, kuma bayan binciken da ya gudanar ya gano cewa wurin aikin mallakin Gwamnatin Jihar Neja ne. Hakan ne ya sa ya nemi haɗin kan Ƙungiyar NUMW domin gudanar da aikin bisa doka.

A cewarsa, tsarin rabon abin da aka haƙo zai kasance ne bayan an ware haƙƙin ma'aikatan haƙar ma'adinai, sannan gwamnati, kamfanin da ƙungiyar su raba kaso kamar yadda yarjejeniyar ta tanada. Ya bayyana cewa za a yi lissafin abin da aka samu duk bayan wata guda, inda za a raba ma'adinan kai tsaye maimakon biyan kuɗi.

Ana sa ran wannan shiri zai taimaka wajen bunƙasa tattalin arziki, samar da ayyukan yi da kuma tabbatar da gudanar da harkar haƙar ma'adinai cikin tsari da bin doka a Jihar Neja.

A ƙarshe, Ƙungiyar NUMW ta yaba wa Gwamnatin Jihar Neja da Ma'aikatar Kula da Albarkatun Ƙasa ƙarƙashin jagorancin Kwamishina, Hon. Mohammed Qasim Danjuma, bisa wannan yunƙuri na inganta harkar ma'adinai a jihar.

Post a Comment

Previous Post Next Post