Labarai

Gidauniyar Ƙarfafa Matasa Ta Horar Da Matasa Da Mata Kan Dogaro Da Kai A Zariya

Daga Idris Umar, Zariya

Gidauniyar Ƙarfafa Matasa (Inspire Youth for the Nation Foundation), ƙarƙashin jagorancin shugabanta, Injiniya Ridwan Mika'il Fagaci, tare da haɗin gwiwar Global Hub Ventures, ta shirya taron horaswa na yini guda domin bai wa matasa da mata ilimi da ƙwarewa kan harkokin noma na zamani, kasuwancin dijital da kiwon dabbobi.

An gudanar da taron ne ƙarƙashin taken "Youth Mentorship", inda aka mayar da hankali kan horas da matasa da mata daga Ƙaramar Hukumar Soba ta Jihar Kaduna domin ƙarfafa musu gwiwa wajen dogaro da kai da bunƙasa tattalin arzikinsu.

An gudanar da taron a babban ɗakin taro na Cibiyar Bincike da Yaɗa Fasahohin Noma ta Ƙasa (NAERLS) da ke Jami'ar Ahmadu Bello (ABU), Zariya, tare da samun halartar shugabannin matasa, wakilan ɗalibai daga jami'ar da sauran masu ruwa da tsaki daga Ƙaramar Hukumar Soba.

A yayin taron, mahalarta sun samu horo kan dabarun noma na zamani, kasuwancin dijital da hanyoyin kiwon dabbobi cikin inganci. Masana sun yi bayanin yadda waɗannan fannoni za su taimaka wajen samar da ayyukan yi, rage zaman banza da kuma inganta rayuwar matasa da mata.

Da yake jawabi, Shugaban Gidauniyar Ƙarfafa Matasa, Injiniya Ridwan Mika'il Fagaci, ya yaba wa mahalarta bisa yadda suka amsa gayyata tare da nuna ƙwazo wajen neman ilimi.

Ya ce koyar da matasa sana'o'i da dabarun kasuwanci na zamani na daga cikin hanyoyin da za su taimaka wajen rage rashin aikin yi da kuma samar da ci gaba mai ɗorewa a cikin al'umma.

Injiniya Fagaci ya kuma yi kira ga shugabannin siyasa da masu riƙe da muƙaman gwamnati da su ba shirye-shiryen bunƙasa rayuwar matasa muhimmancin da ya dace, musamman ta hanyar samar da manufofi da shirye-shiryen da za su inganta walwalar al'umma.

A nasu jawaban, Shugaban Jam'iyyar African Democratic Congress (ADC) na Ƙaramar Hukumar Soba, Alhaji Magaji Kado, da Shugaban Matasan jam'iyyar, sun bayyana cewa wannan shiri ya zo a kan lokaci, domin yana taimakawa wajen gina ƙwarewar matasa da bunƙasa ci gaban al'umma.

Sun yaba wa gidauniyar bisa hangen nesanta, tare da bayyana cewa irin waɗannan shirye-shirye na ƙara wa matasa ƙarfin guiwa wajen dogaro da kai da zama masu amfani ga al'umma.

A matsayin wani ɓangare na shirin, mahalarta sun kai ziyara Cibiyar Binciken Kiwon Dabbobi ta Ƙasa (NAPRI), Shika, da ke Jami'ar Ahmadu Bello, Zariya, inda suka samu horo a aikace kan bincike da hanyoyin kiwon dabbobi na zamani.

An kuma nuna musu sabbin fasahohi da dabarun bunƙasa kiwo, domin su yi amfani da ilimin da suka samu wajen inganta harkokinsu bayan komawa gidajensu.

A ƙarshen taron, an karrama wasu fitattun shugabannin al'umma da lambobin yabo saboda gudummawar da suke bayarwa wajen bunƙasa matasa da ci gaban tattalin arzikin Ƙaramar Hukumar Soba.

Masu shirya taron sun bayyana cewa za su ci gaba da gudanar da irin waɗannan shirye-shirye a sassa daban-daban domin bai wa matasa da mata damar samun ilimi, ƙwarewa da hanyoyin dogaro da kai, tare da taimakawa wajen gina al'umma mai ci gaba da wadata.

Post a Comment

Previous Post Next Post