Yadda Muzaharar Kudus Ta Shekarar 2025 Ta Gudana A Garin Zariya

ƴan uwa Musulmi na Harka musulunci a Najeriya na ci gaba da Alla-wadai akan kisan gillar da haramtacciyar kasar Isra'ila ke ci gaba da aiwatar kullum akan raunanan al'umma ƙasar Falasɗinu  Muzaharar wanda aka yi a yau Juma'a, 28 ga watan Ramadan 1446 daidai da 28 ga Maris, 2025. An ɗauko ta ne daga babban masallacin juma'a na gwargwaje, inda aka rufe ta a rimin ƙwaƙwa da ke cikin birnin Zariya. Muzaharar ta ƙayatar ta yadda al'umma daban-daban maza da mata ko ta ina sun zo, dauke da tutoci da baje da dauke da hotuna iri daban daban waɗanda da ke nuna irin ta'addacin haramtacciyar kasar Isra'ila ga al'umma Falasɗinawa. 

A gefe guda kuma al'umma gari ne ke ta tururuwar fitowa domin ga ne wa idonsu, yadda ƴan uwa Musulmi Almajiran Shaikh Zakzaky ke gudana da Muzaharar ta tir da irin ta'addacin ƙasar Isra'ila akan fararen hula a ƙasar Falasɗinu.  Duk da irin barazanar jami'an tsaron Najeriya, a wajen Muzaharar ƙudus ɗin na bana, an kammala Muzaharar cikin izza har zuwa wajen da aka rufe. Wakilin ƴan uwa Musulmi Almajiran Shaikh Zakzaky a garin Zariya, Shaikh Abdulhamid Bello Zariya ya jagoranci rufe Muzaharar. inda ya gabatar da takaitaccen jawabi akan maƙasudin fitowarsu Muzaharar ta Ƙudus. Kana ya ya yi albishir ga al'ummar Musulmi da su ƙara jajircewa wajen goyon bayan al'umma Falasɗinu da ma sauran al'ummar musulmin duniya, wanda azzalumai ke ci gaba da zalinta kullum a faɗin duniya. "ta'addacin ƙasar Isra'ila na gab da zamowa tarihi a doron ƙasa baki ɗaya". 

Daga karshe, Shaikh Abdulhamid ya yi Alla-wadai ɗin sa dangane da irin ta'addacin ƙasar ta Isra'ila ga raunana Falasɗinawa. Ita dai wannan Muzahara, Jagoran juyin juya halin Musulunci a Iran, Ayatullah Imam Ruhollah Khomeini ne ya ayyana ranar Juma'ar ƙarshe na watan Ramadan a matsayin ranar Qudus ta duniya domin al'umma masu neman adalci a duniya su tunkari zalunci tare da nuna goyon baya ga gwagwarmayar Falasɗinawa.  

A Najeriya, Kusan shekaru arba’in ke nan Harkar Musulunci tana gudanar da wannan muzaharori a irin wannan rana, duk da hare-haren da take fuskanta daga mahukumta. Muzaharar wacce ake yi duk shekara domin nuna goyon baya ga al’ummar Falasɗinu tare da kuma yin tir da zaluncin da haramtacciyar ƙasar Isra’ila ke aikatawa a kodayaushe. An gudanar da muzaharori ne a dukkannin jihohin Nijeriya, ciki har da Babban Birnin Tarayyar Najeriya. 


Hoto: Elbataky 4tos Zariya 

- Salisu Jibril Khidir 

28032025

Post a Comment

Previous Post Next Post