Gwamnan jihar Kano a arewacin Najeriya ya kafa kwamatin da zai bincika yadda aka yi game da ƙorafin da wasu ma'aikatan jihar ke yi na ƙin biya ko kuma yanke musu albashi a watan Janairu. Abba Kabir ya bayyana lamarin da "take haƙƙin ma'aikata da kuma ha'intar jama'a", kamar yadda wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a yau Alhamis.
"Wannan gwamnatin ba za ta taɓa yarda da rashin adalci ga ma'aikatanmu ba, kuma duk wanda aka samu da laifi zai fuskanci fushin hukuma," kamar yadda sanarwar ta ruwaito gwamnan na faɗI.
An umarci kwamatin ya gudanar da "cikakken bincike" kan tsarin biyan albashi na gwamnatin jihar don gano "ko kuskuren na'ura ne ko kuma da gangan", sannan ya ba da shawarar matakin da za a ɗauka. Kwamatin ya ƙunshi jami'an gwamnati 10 ƙarƙashin jagorancin Abdulkadir Abdussalam, wanda shi ne kwamashinan raya karkara da cigaban al'umma.

Post a Comment