Hijira 1448: Za a Samu Yalwar Tattalin Arziƙi a Nijeriya – Sheikh Muhajjadina


Daga Bello Hamza, Abuja

A yayin da al’ummar Musulmi a duniya ke murnar shiga sabuwar shekarar Hijira ta 1448, an yi hasashen cewa, duk da ƙalubalen da duniya za ta fuskanta a fannin tattalin arziƙi, Nijeriya za ta samu yalwa da ƙarin bunƙasar tattalin arziƙi a tsakanin talakawa.

Wannan hasashe ya fito ne daga bakin Sheikh Muhajjadina Sani Kano Al-Falaki, wanda kuma ya bayyana kansa a matsayin shugaban masu ilimin taurari na nahiyar Afirka, a wata tattaunawa da Wakilinmu ta wayar tarho daga birnin Makka.

Bayanai sun nuna cewa, a duk farkon sabuwar shekarar Musulunci, Sheikh Muhajjadina kan bayyana hasashen da bincikensa ya nuna game da yadda muhimman al’amura za su kasance a cikin shekarar. Ya ce za a iya samun rikice-rikice tsakanin ƙasashen duniya, tare da matsalolin tattalin arziƙi da ƙarin saɓani; sai dai kuma wasu ƙasashe za su samu ci gaba mai kyau a fannin tattalin arziƙi.

Ya ƙara da cewa za a samu sabbin masu arziki a wannan shekara, yayin da ƙasashe masu ƙarfi za su yi ƙoƙarin mamaye wasu ƙasashe, amma hakan ba zai cika ba. Ya kuma ce za a iya samun rashe-rashen manyan mutane masu iko a wasu ƙasashe, tare da bullar sabbin cututtuka a wasu yankuna, sai dai ya ce “ba za a iya bayyana sunayensu ba saboda wasu dalilai.”

Ya ce:

“Alhamdulillahi, Musulunci zai ƙara samun karɓuwa da ci gaba sosai a wannan shekara. Haka kuma, mutane masu cikin ƙunci da damuwa za su samu sassauci daga duk inda suke a duniya.”

Ya kuma ƙara da cewa:

“Buwaya da ƙima ta ‘yan ƙasa za ta ɗan motsa a wannan shekara. Haka kuma, masu neman mukamai ko ci gaba a ayyukansu, kamar samun ƙarin girma (promotion), da yawa za su cimma burikansu.”

Ya kuma yi gargaɗi cewa ya kamata mutane su kula da dukiyoyinsu, domin darajar kuɗi na iya raguwa a wani lokaci, sannan dawo da abin da aka rasa na iya zama da wahala.

A cewarsa, za a kuma samu ƙarin saɓani a tsakanin ma’aurata da masoya, wanda ka iya haifar da rabuwar aure da dama. Don haka ya buƙaci mutane da su riƙa haƙuri da juriya a zamantakewarsu.

Ya ƙara da cewa, duk da yanayin ƙalubale, akwai wuraren da mutane za su samu farin ciki da sauƙin rayuwa, in sha Allahu.

Sheikh Muhajjadina ya kuma ce za a samu yawaitar ciwon kai, ciwon mara da ciwon ciki a tsakanin al’umma a wannan shekara.

Ya kuma yi gargaɗin cewa za a samu yawaitar karya alƙawura da batun bashi da lamuni, inda ya shawarci mutane da su guji ba da kuɗi mai yawa a matsayin bashi, sai dai a taimaka da abin da za su iya a matsayin kyauta.

Dangane da zaɓen 2027, Sheikh Muhajjadina ya ce za a gudanar da zaɓe lafiya ba tare da manyan tashin hankali ba, sai dai za a samu rikice-rikice a lokacin yaƙin neman zaɓe. Ya ce ‘yan siyasa da dama za su yi asara, wasu kuma za su cimma nasara.

Ya kuma yi gargaɗi ga jami’an tsaro da ‘yan siyasa da su yi aiki cikin ƙwazo da gaskiya, domin rage tashe-tashen hankula. Ya ƙara da cewa ana iya samun ƙaruwar sace-sacen manyan jami’an gwamnati da ‘yan siyasa.

Haka kuma ya ce wasu ƙasashen Afirka na iya fuskantar juyin mulki da tashin hankali, kamar yadda aka gani a shekarar da ta gabata.

A fannin tattalin arziƙi kuma, ya ce bincikensa ya nuna cewa za a samu ɗan matsin tattalin arziƙi a farko, amma daga baya arziƙi zai yalwata. Farashin kayayyaki zai sauka, kuma mutane da dama za su samu sauƙin rayuwa. Wasu za su ƙara arziki, yayin da wasu kuma za su fuskanci raguwar dukiya a cikin shekarar.

Ya kuma shawarci shugabanni da su riƙa nuna tausayawa ga talakawa, domin matsin rayuwa ga jama’a na iya haifar da rikice-rikice idan ba a kula ba.

A ƙarshe, ya buƙaci al’umma gaba ɗaya da su riƙa neman bayani daga masana ilimin taurari domin fahimtar yadda al’amura ke tafiya, don kauce wa shiga halin da zai iya shafar rayuwarsu da harkokinsu.

Post a Comment

Previous Post Next Post