CIKAKKEN RAHOTON YADDA MUZAHARAR QUDUS TA GUDANA A ABUJA

 


Kamar yadda aka sani yau Harkar Musulunci ta gudanar da Muzaharar Qudus a Abuja da sauran garuruwan Najeriya kamar yadda ta fitar a sanarwan daya gabata. An fara muzaharar Qudus bayan idar da sallah a masallacin Banex plaza, sannan aka taho da muzaharar har junction din Banex din, duk jami'an tsaro na biye da muzaharar, anzo junction sun tsaya suka tare hanya suka yi harbi a sama, amma matasa suka wuce suka cigaba da muzaharar su.

 Sai sojojin dake biye da muzaharar suka taso wata Tanka da suke ta kokarin daman sai sun sha kan muzaharar da ita tun fara muzaharar basu samu hanya ba, sai sukazo suka shige gaban muzaharar juyawan da zasuyi gaban muzaharar da tankar sai kawai suka bude wuta kan masu muzaharar" sai matasan suka fara kabbara suka tinkari azzaluman, sannan kuma akwai wasu sojoji a cikin mota hiloz guda biyu su Kuma suna junction din Banex din suna bayan muzaharar kenan, bayan wadancan sojojin sun bude wuta ta gaban muzaharar sai su wanda suke bayan suka bude wuta, harbi gaba da baya. Tunda ake muzahara a Abuja basu taba harbi irin na yau ba, gaba ana harbi baya ana harbi an saka 'yan uwa a tsakiya. 

Bayan sun bude wuta sun kashe mutane sosan gaske, wasu an samu damar daukar gawar tasu wasu kuma da ake tsammanin sama da mutum goma su sojojin da suka kashesun sun dauki gawar tasu, sannan sun harbi 'yan uwa da dama anyi nasarar daukar wasu, suma jahiliyan da sukayi kisan sun debi wanda suka harba sama da mutum 15, sannan kuma bayan tarwatsa muzaharar sun cigaba dabin 'yan uwa suna kamasu wanda ake zargin sun kama 'yan uwa sama da mutum 100, har zuwa daren nan da muka hada wannan rahoton 'yan uwa ne ke dawowa daga cikin garin   Abuja, kuma zuwa hada wannan rahoton bayanin da mukayi shine takaitaccen abun da muka sani, idan akwai wani abu zamu rubuta daga baya.


Isa Charis 

Ali Assajjad Ibn Taheer

 28th March/ 2025

Post a Comment

Previous Post Next Post