Maigana Ya Sanar Da Tsayawa Takarar Majalisar Wakilai Ta Tarayya A Karkashin Jam'iyyar NDC

Daga Idris Umar, Zariya

Fitaccen matashin ɗan siyasa daga Ƙaramar Hukumar Soba ta Jihar Kaduna, Hon. Abdullahi Allow Maigana, ya sanar da aniyarsa ta tsayawa takarar kujerar Majalisar Wakilai ta Tarayya domin wakiltar mazaɓar Soba/Maigana a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar National Democratic Coalition (NDC).

Da yake zantawa da manema labarai, Hon. Abdullahi Allow ya bayyana cewa ya fice daga jam'iyyar PDP zuwa NDC ne domin kawo sabon salo na siyasa wanda zai haifar da ci gaba mai ɗorewa ga al'ummar Ƙaramar Hukumar Soba.

Ya ce ya shafe shekaru da dama yana fafutukar siyasa, inda ya taɓa tsayawa takara tare da riƙe muƙamai daban-daban a jam'iyyar PDP, amma ya yanke shawarar sauya tafiya domin ya fi bai wa al'umma ingantacciyar wakilci.

A cewarsa, babban burinsa shi ne inganta rayuwar al'ummar mazaɓar ta hanyar samar da ci gaba mai ɗorewa da magance matsalolin da suke fuskanta.

Hon. Abdullahi Allow ya yi alƙawarin cewa idan aka zaɓe shi, zai mayar da hankali wajen samar da ayyukan yi ga matasa, bunƙasa ilimi da harkokin lafiya, inganta tsaro, tare da ƙarfafa harkokin noma da kiwo, waɗanda ya bayyana a matsayin ginshiƙan tattalin arzikin yankin Soba.

Haka kuma, ya yi alƙawarin bai wa mata dama ta hanyar shirye-shiryen ƙarfafa tattalin arzikinsu da kuma ƙara musu damar taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban al'umma.

Ya kuma buƙaci magoya bayan jam'iyyar NDC da su kasance jakadu nagari ta hanyar wayar da kan jama'a kan manufofi da shirye-shiryen jam'iyyar cikin lumana da bin doka.

Bugu da ƙari, ya yi kira ga matasa da su ci gaba da kasancewa masu zaman lafiya tare da mara wa jam'iyyar NDC baya domin tabbatar da sauyin da al'ummar Soba ke fata.

A nasa jawabin, Shugaban jam'iyyar NDC na Ƙaramar Hukumar Soba, Hon. Yayo, ya bayyana cewa jam'iyyar za ta ci gaba da aiki tuƙuru domin samun nasara a zaɓe mai zuwa, yana mai nuna kwarin gwiwar cewa za su yi nasara da yardar Allah.

Ita ma Shugabar Mata ta jam'iyyar NDC a Soba, Molina Jonathan, ta ce mata da maza a faɗin ƙaramar hukumar sun shirya tsaf domin mara wa jam'iyyar baya saboda manufofinta na ci gaba da inganta rayuwar al'umma.

Hakazalika, Shugaban Matasan NDC na Ƙaramar Hukumar Soba, Abubakar Raiyanu, ya tabbatar da cikakken goyon bayan matasa ga Hon. Abdullahi Allow Maigana, yana mai cewa sun gamsu da hangen nesansa da ƙudurinsa na kawo ci gaba ga al'umma.

Taron ya nuna ƙoƙarin jam'iyyar NDC na faɗaɗa tasirinta a Ƙaramar Hukumar Soba, inda shugabanni da mambobinta suka bayyana fatan samun gagarumar nasara a zaɓe mai zuwa.

Post a Comment

Previous Post Next Post