An Rufe Tafsirin Alkur'ani Mai Girma Na Watan Ramadan 1446 A Da'irar Zariya


Bayan shafe kwanaki 29 , yan uwa Musulmai Almajiran Sayydi Zakzaky (H) na garin Zariya suna gudanar da Tafsirin Alqur'ani mai girma na watan Ramadan É—in Shekarar 2025 = 1446, A yammacin yau Alhamis 27 ga watan Ramadan 1446, dai dai da 27 gawatan Maris 2025 sun rufe Tafsirin na wannan shekarar. 

Kamar yadda saba a tsawan kwanakin karatun Tafsirin , an kebe ranakun Talata don gudanar da karatun Ahlaq cikin littafin Ahlaqu Ahlil Bait . sannan kuma a dukkan ranakun Lahadi da Alhamis ana gabatar da MUHADARA akan Maudu'ai daban daban. Don haka ne ma a zaman na yau wato ranar rufewar an gudanar da MUHADARA ne mai taken taken : "Masallacin Qudus Da Al'umman Palastinu" wanda Farfesa Abdullahi Dalladi na Jami'ar Ahmadu Bello dake Zariya ya gabar da jawabi akai. 

Acikin jawabin sa ''Farfesan yayi bayani tiryan tiryan akan Masallacin Qudus , matsayin sa a Muslunci da wurin Musulmai da irin halin da yake ciki a yanzu. Hakanan yayi bayanin Falastinawa rayuwar su gwagwarmayar su ,  halin dasuke ada , da yadda suka kawo a yanzu. Ya kuma yi karin haske akan yadda Marigayi Imam Khumaini (Q.S) ya Assasa ranar Juma'a ta karshe Ramadan matsayin ranar Qudus na duniya (Ranar Raunana).   

Sannan kuma ya nuna takaicinsa  na yadda ko ina a duniya anayin ranar Qudus lafiya amma banda Nigeria ko kuma jihar kaduna da Zariya.  Inda yace hatta dabbobin daji anga yadda suka nuna goyan bayan su ga Falastinawa  da kuma kinsu da zaluncin yahudawan Izra'ilawa A yayn gabatar da ta'alikin sa , Sheikh Abdulhamid Bello ya jaddada fitowar yan uwa muzaharar Qudus Gobe , ya kuma bukaci yan uwa  da zama cikin tsari da bin nizami, wanda in anyi hakan za'a samu nasara.  Ya kuma nemi yan uwa da suyi amfani da wannan dare na Juma'a wajen karin niman kusanci da Allah kowa yafito cikin kyakkyawan niyya. 

Ya karkare da bayani akan muhimman Ayyukan da akeyi ranar Idi . Kamar Zakkatul Fitri , wanda yahau kan dukkan magidanci. Hakama sallan idi wanda sunna ne da mutum zai iyayi koda shi kadai ne. Akarshe anyi addu'a na musamman ga Jagora da sauran yan uwa,  musamman yadda yan uwa suka daure wajen halartar karatun tsawan kwanuka da akayi. Daga kasa wasu daga cikin hotunan yanda zaman ya gudana ne a yammacin yau din

Post a Comment

Previous Post Next Post