Majalisar dokokin ƙasar Senegal ya ɗage kariyar majalisar kan wasu mambobinta biyu, da ake zargi da ɓarnatar da kuɗaɗen gwamnati da aka ware don yaƙi da annobar Corona.
Moustapha Diop ya kasance ministan masana'antun ƙasar, yayin da Salimata Diop ke matsayin ministar mata a ƙarƙashin gwamnatin tsohon shugaban ƙasar Macky Sall.
Tuni dai ƴan majalisar suka musanta zargin da ake yi musu. Aƙalla ministoci shida ƙarƙashin tsohuwar gwamnatin aka zarga da cin hanci da rashawa da ya kai dala biliyan ɗaya da rabi. Shugaban ƙasar Bassirou Diomaye Faye da aka zaɓa a shekarar 2024 ya alƙawarta magance matsalar cin hanci da rashawa a ƙasar.

Post a Comment