Daga Aqil Abdulkadir
An gudanar da jana'izar Hajiya Raliya Ahmad, mahaifiyar Babban Limamin Zazzau, Malam Ɗalhatu Kasim Imam, da yammacin ranar Talata a birnin Zariya.
Marigayiyar ta rasu ne a ranar Talata bayan fama da jinya. An gudanar da sallar jana'izarta da misalin ƙarfe 5:30 na yamma, inda Babban Limamin Zazzau, Malam Ɗalhatu Kasim Imam, ya jagoranci sallar.
Mai Martaba Sarkin Zazzau, Amb. Malam Ahmed Nuhu Bamalli, CFR, tare da manyan malamai, hakimai da ɗimbin al'umma ne suka halarci jana'izar, wadda aka gudanar a maƙabartar da ke kusa da gidan Babban Limamin a Unguwar Juma, cikin birnin Zariya.
Masu halartar jana'izar sun yi addu'ar Allah Ya gafarta wa marigayiyar, Ya jikanta da rahama, Ya sanya Aljannatul Firdausi ta zama makomarta, tare da bai wa iyalanta da sauran 'yan uwa haƙurin jure wannan babban rashi.
Post a Comment