Amnesty International Ta Nemi A Sake Sakin Omoyele Sowore Nan Take


Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam ta Amnesty International Nigeria ta yi kira ga gwamnatin Nijeriya da a saki  fitaccen ɗan gwagwarmaya kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Omoyele Sowore nan take ba tare da wani sharaɗi ba bayan kotu ta bayar da umarnin a tsare shi a Abuja.

Ƙungiyar ta bayyana cewa ma’aikata, magoya baya da masu fafutuka na Amnesty International sun halarci zaman kotun domin nuna goyon baya ga Sowore, wanda ta ce hukumomin Nijeriya na ci gaba da kai masa hari saboda bayyana ra’ayinsa kan rashin adalci da kuma neman a yi gaskiya da riƙon amana a shugabanci.

Amnesty International ta ce tsare Sowore ya saɓa doka, tana mai cewa ana tsare da shi ne kawai saboda ya yi amfani da ‘yancinsa na faɗin albarkacin baki, wanda ya haɗa da ‘yancin bayyana ra’ayi.

Ƙungiyar ta ƙara da cewa wannan mataki na nuna yadda ake rage sararin ‘yancin al'umma a Nijeriya, tare da ƙara tsaurara matakan takura wa masu fafutukar kare haƙƙin ɗan Adam da ‘yancin faɗin albarkacin baki.

A ƙarshe, Amnesty International ta yi kira ga hukumomin Nijeriya da su bi ƙa’idojin dokokin ƙasa da ƙasa, tare da tabbatar da kare ‘yancin ‘yan ƙasa na bayyana ra’ayi, taro cikin lumana, kafa ƙungiya da kuma ‘yancin kafafen yaɗa labarai.

Post a Comment

Previous Post Next Post