Manzon Allah (S) Ya Yi Wasiya Da Jagorancin Imam Ali (A.S) - Jagora Sheikh Zakzaky


Daga Ofishin Jagora Sheikh Ibraheem Zakzaky (H)

A yau Alhamis, 18 ga Zhul Hijja 1447, Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) ya gabatar da jawabin ranar Ghadeer, ranar da Manzo (S) ya nasabta Imam Ali (A.S) a matsayin magajinsa, ga É—imbin mahalarta daga sassa daban-daban a Abuja.

Da yake jawabi, ya bayyana Ghadeer a matsayin babbar rana mai muhimmanci a Musulunci. Ya bayyana cewa, huɗubar Ghadeer, wasiyar Manzon Rahama (S) ce da ta ƙunshi muhimmin umurni da jagoranci ga al'ummar Musulmi. Ya ƙara da cewa, nasabta Imam Ali da Ahlul Baiti umurnin Allah ne, kuma bin wannan umurnin ne tsira. Ya ce, "Manzon Allah (S) ya yi wasiya, kuma wajibin ka ne ka bi, in ba ka bi ba, za ka haɗu da Allah." Ya ci gaba da cewa, "Gwaji ne (ake mana), an gwada na farko, kai ma ana gwada ka ne."

Ya jaddada cewa, Ghadeer a Musulunci ba ɓoyayyen abu ba ne. Duk da dai an yi ƙoƙarin rufe shi, amma a sarari yake kamar hasken rana. Ya kawo cewa, babu wani hadisi da ya kai haddin 'tawatir' a duniyar Sunna da Shi'a kamar hadisin Ghadeer. Daga ƙarshe, ya yi addu'ar Allah Ya nuna mana bayyanar Imam Mahdi (AS), wanda da bayyanarsa ne za a koma ga ainahin koyarwar addinin Musulunci.

@Szakzakyoffice 
#EidMubarak 
#FreePalestine 
#PrayForPalestine 
#OurImmortalHeroes 
18/DhulHijja/1447
04/06/2026

Post a Comment

Previous Post Next Post