Daga Idris Umar, Zariya
An gudanar da ƙaddamar da shirin
'Maicanter Micro Personal Empowerment Scheme 1.0' a harabar Sakatariyar Karamar
Hukumar Zariya, inda ya samu gagarumar karɓuwa daga al’umma.
Shirin wanda Sakataren Karamar
Hukumar Zariya, Hon. Alhaji Shuaibu Abdullahi Maicanter, ya assasa a ƙarƙashin
tafiyar jam’iyyar APC, an tsara shi ne domin ƙarfafa tattalin arziƙin al’umma
da rage talauci ta hanyar tallafawa jama’a kai tsaye.
A yayin taron, an raba tallafi ga
fiye da mutum 700 daga sassa daban-daban na Ƙaramar Hukumar Zariya, inda suka
amfana da kayayyaki da kuɗaɗen da za su taimaka musu wajen inganta rayuwarsu da
harkokinsu na yau da kullum.
Daga cikin abubuwan da aka raba akwai
motoci, babura, kekuna, injinan gyaran tayoyi (vulcanizing machines), injinan ɗinki,
buhunan kayan abinci, galan-galan na man gyada, da kuma tallafin kuɗi ga mata.
Haka kuma, an bai wa wasu daga cikin
masu buƙata ta musamman kekunan guragu domin sauƙaƙa musu zirga-zirga.
Bugu da ƙari, wasu daga cikin waɗanda
suka ci gajiyar shirin sun samu guraben tallafin karatu, yayin da aka ware
guraben Umrah guda goma domin ƙara ƙarfafa ɓangaren addini da zamantakewa.
Shirin ya samu halartar manyan baki
da suka haɗa da shugaban ALGON na Jihar Kaduna, Hon. Abubakar Jamil Albani
Samaru, Hon. Baba Isa, da Shugaban Karamar Hukumar Zariya, Hon. Jaga, inda suka
yabawa shirin tare da jaddada muhimmancinsa wajen bunƙasa rayuwar jama’a.
A nasu jawabai, sun nuna goyon baya
ga mai shirin tare da jinjinawa Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, da
Kakakin Majalisar Wakilai ta Tarayya, Hon. Abbas Tajuddeen, bisa ƙoƙarin su na
inganta rayuwar al’umma.
Wasu daga cikin waɗanda suka ci
gajiyar shirin sun bayyana farin cikinsu, inda suka ce tallafin zai taimaka
musu wajen dogaro da kai da inganta sana’o’insu.
Da yake zantawa da manema labarai
bayan kammala taron, Hon. Maicanter ya gode wa Allah tare da yabawa shugabanni
daban-daban bisa goyon bayan da suke ba shi, inda ya sha alwashin ci gaba da
kawo shirye-shiryen da za su amfani al’umma.
An kammala taron cikin nasara, inda
aka fara lafiya aka kuma tashi lafiya.

Post a Comment