Daga Abdullahi Idris, Bauchi
Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed, ya hori sabbin jami'an rundunar Forest Guard Corps 2,187 da aka yaye da su gudanar da aikinsu cikin ƙwarewa, ladabi da kuma mutunta haƙƙin ɗan Adam domin tabbatar da tsaro a faɗin jihar.
Gwamnan ya bayar da wannan shawara ne yayin bikin yaye sabbin jami'an da aka gudanar a Makarantar Horar da 'Yan Sanda da ke Yelwa, ƙaramar hukumar Bauchi.
Mataimakin gwamnan jihar, Hon. Auwal Jatau, ne ya wakilci Gwamna Bala Mohammed a wajen bikin.
A cikin saƙonsa, gwamnan ya taya sabbin jami'an murnar kammala horon makwanni biyu da suka yi, tare da bayyana cewa an shirya horon ne domin samar da jami'an tsaro masu nagarta da za su taimaka wajen kare dazuzzuka da kuma tabbatar da zaman lafiya.
Ya buƙaci sabbin jami'an su kasance jakadu nagari na jihar, su gudanar da aikinsu cikin gaskiya, riƙon amana da bin ƙa'idojin aiki, yana mai jaddada cewa rundunar Forest Guard Corps an kafa ta ne domin ƙarfafa zaman lafiya da kare muhalli.
Gwamnan ya kuma yi gargaɗin cewa gwamnatin jihar ba za ta lamunci duk wani saɓa wa doka ko cin zarafin jama'a ba, tare da ƙarfafa musu gwiwar su yi aiki cikin bin ƙa'idojin da aka shimfiɗa.
A nasa jawabin, Babban Kwamandan Hukumar 'Yan Banga da Ƙarfafa Matasa ta Jihar Bauchi, Umar Aliyu Shayi, ya yabawa Gwamna Bala Mohammed bisa ƙoƙarinsa na bunƙasa hukumomin tsaro na cikin gida domin inganta tsaron rayuka da dukiyoyin al'umma.
Ya kuma buƙaci sabbin jami'an da su kasance masu jajircewa, biyayya da sadaukar da kai wajen gudanar da ayyukansu.
Haka nan, Shayi ya yaba da kyakkyawar haɗin gwiwar da ke tsakanin hukumomin tsaro daban-daban a jihar, yana mai tabbatar da cewa hukumar 'yan banga za ta ci gaba da aiki tare da sauran jami'an tsaro domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a faɗin Jihar Bauchi.

Post a Comment