Yadda Aka Gudanar da jana'izar shahidan waki'ar Kudus na Abuja a Zariya


A safiyar ranar Lahadi 1 ga watan Shauwal 1446, daidai da 30 ga watan maris ne, yan uwa , Musulmi Almajiran Sayyid Zakzaky (H) dake garin Zaria suka gudanar da Jana'izar Shahidan Qudus na Abuja su shida. Jana'izar ta gudana ne jim kadan bayan kammala sallar idi wacce akayi a mullin makarantar Fuddiya dake Zaria . 

Su dai Shahidan da aka gudanar da Jana'izar tasu, sun rasa rayuwar su ne a ranar Juma'ar da ta gabata 28/03/2025 , sakamakon afka musu da jami'an tsaron Soji suka yi da rana tsaka a garin Abuja. Laifin su kawai shine sun fito Muzaharar Nuna Goyon bayan ga Al'ummar Ƙasar FalasÉ—inu, wanda suka saba yi a duk shekara, A duk Juma'an Ƙarshen watan Ramadan.  A wannan shekarar fitowar su keda wuya, kawai jami'an tsaron Sojin suka buÉ—e musu wuta da harsasai masu rai,  inda nan take su mutane shidan suka rasa ransu. Suka kuma kama mutane 284 maza da mata cikin su harda masu raunukan harbi su 20.

Wakilin 'Yan Uwa Nagarin Funtua; Shaikh Rabi'u ne ya Jagoranci Jana'izar inda bayan an kammala Sallar aka wuce dasu Darur Rahama aka rufe su, dubbun nan yan uwa mata da maza ne suka samu halarta, yayin jawabin sa a wurin bayan kammala jana'izar Sheikh Rabi'u Funtua, ya baiyana cewa su shahidai suna kara jaddada mana maganar da aka fada mana ne akan tafiyar nan, cewa a cikin ta akwai mutuwa akwai kamu akwai É—auri, don haka mu kuma muna kara jaddada musu cewa, tabbas ba zamu basu kunya ba wannan hanyar da aka kashe su kanta muma muna nan kanta, ba zamu taÉ“a sanjawa ba koda ko za a karar damu duka, balle ma bazai taÉ“a yuyuba karar damu duka ba. Ya kuma jaddada ma mahukuntar Nigeria cewa kisa da kamu ba zasu taÉ“a hanamu addini ba har abada, su suna nasu mu ma kuma muna namu . Bayan ya kammala ne wakilin yan uwa na Zaria Sheikh Abdulhamid Bello ya rufe taron da addu'a aka sallami mutane 

An fara lafiya an kuma kammala lafiya . Daga kasa wasu daga cikin hotunan yanda jana'izar ta gudana ne


Post a Comment

Previous Post Next Post