Shirin Makon Ɗanfodiyo na shekarar 2026 wanda dandalin ɗalibai da malamai na Harkar Musulunci ƙarƙashin jagorancin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) suka shirya, ya gudana tun daga ranar Juma’a 24 ga watan Afrilun 2026 zuwa Lahadi 26 ga watan Afrilun, cikin nasara a jihohi da dama na Najeriya, tare da haɗa ayyukan wayar da kai, ziyartar wuraren tarihi, da kuma tarukan ilimi da ayyukan ibada.
Rana ta Farko: Gangamin Wayar da Kai
An fara shirin da gangamin wayar da kai a Jihar Sakkwato, inda aka gudanar da shi a jami’ar Usmanu Danfodiyo (UDUS) da kuma jami’ar jihar Sakkwato (SSU). An raba maƙaloli tare da ilmantar da ɗalibai da ma’aikata kan muhimmanci da manufofin Makon Ɗanfodiyo.
A Jihar Kebbi, Dandalin (AFIM) ta gudanar da irin wannan gangami a shirin da aka kira ‘Gwandu Emirate Orientation Program’ a harabar jami’ar AFUSTA, inda aka raba takardu ga mahalarta daga ƙananan hukumomi goma.
Haka kuma a Zariya, reshen makarantar ECAS ya raba makaloli ga ɗalibai a ranar 24 ga Afrilu, 2026. A Kaduna, an kai gangamin a Al-Mannar Mosque Unguwan Rimi Kaduna, sannan aka ci gaba a jami’ar jihar Kaduna (KASU) ta hanyar liƙa makaloli da raba su ga ɗalibai.
A Jihar Katsina kuwa, reshen jami’ar Umaru Musa Yar’adua ya raba maƙaloli kan makon a Babban Masallacin jami’a tare da liƙa makaloli a wurare daban-daban na harabar makaranta.
Rana ta Biyu: Ziyartar Wuraren Tarihi da Hubbaren Shehu
A rana ta biyu, an kai ziyara zuwa Dagyel a Sakkwato—wani wuri mai muhimmanci da ke da alaƙa da farkon tafiyar ilimi da gyara na Usman Ɗanfodiyo. Mahalarta sun zagaya wuraren tarihi kamar Halwa (wurin khalwa), wurin alwala, masallacin Shehu da rijiyarsa, inda masana tarihi suka gabatar da bayanai kan muhimmancinsu.
Ziyarar ta samu halartar Sheikh Sidi Munir Sakkwato. Mahalarta sun yi muhawara tare da ɗaukar darussa kan adalci, ilimi da gyaran al’umma.
A yammacin ranar, an kai ziyara zuwa hubbaren Shehu a Sakkwato, inda aka gudanar da addu’o’i da nazari mai zurfi, tare da jaddada muhimmancin koyi da koyarwar Shehu Danfodiyo.
Rana ta Uku: Taron Ilimi da Lakcoci
A rana ta uku, an soma gudanar da taro ne da safe, inda Malam Buhari Shehu Wurno ya gabatar da lakca mai taken:
“Da’awar Shehu ƙabilanci ko ta Fata: Fahimtar karantarwar Shehu Usman Ɗanfodiyo wajen kawo gyara da farfaɗo da darajojin Musulunci a Yammacin Sudan.”
Ya yi cikakken bayani kan tarihin Shehu tun daga haihuwa, neman ilimi, jihadi har zuwa kafuwar Daular Usmaniyya. Taron ya samu halartar wakilin ƴan uwa Almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky na yankin Sakkwato, Sheikh Sidi Munir Mainasara da sauran mahalarta.
A zaman yamma, Dr. Shamsudeen Hassan ya gabatar da lakca mai taken:
“Ragowar Gadon Usman Ɗanfodiyo a Yammacin Afirka: Darussa ga Al’ummar Musulmi na wannan Zamani.”
Laccar ta haskaka yadda karantarwarsa da abin da ya kafa ke ci gaba da tasiri, tare da darussan da suka dace da al’umma a yau.
Rana ta Huɗu: Ranar Rufewa
A ranar ƙarshe, an gudanar da zaman tattaunawa kan maudu’i: “Nazarin Siyasar Duniya a Yau: Abubuwan da ke faruwa a Gabas ta Tsakiya, Darussa ga Afirka,” tare da Dr. Shamsuddeen Hassan Zuru, wanda ya yi sharhi mai zurfi kan al’amuran duniya.
Bayan haka, an gabatar da jawabin rufewa daga bakin jagora, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), wanda ya gabatar daga gidansa a Abuja ta hanyar majigi, wanda wannan ya kawo ƙarshen taron cikin nasara.
Kammalawa
Gaba ɗaya, Makon Ɗanfodiyo na shekarar 2026 ya kasance mai cike da nasara, ilmantarwa da haɗin kai. Taron ya wayar da kai dangane ilimi, tarihi da yi don Allah, tare da ƙarfafa fahimtar karantarwar Shehu Usman Ɗanfodiyo da muhimmancin ɗaukar darussa daga rayuwarsa domin gyaran al’umma.
© Dandalin yaɗa labarai na Harkar Musulunci

Post a Comment