Daga Ofishin Sayyid Ibraheem Zakzaky (H)
Da yammacin ranar Alhamis 21 ga watan Shawwal 1447 (9/4/2026) Jagoran Harka Islamiyya, Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) ya jagoranci gudanar da addu'a da taron jajen cika kwanaki 40 Da Shahadar Sayyid Qa'id Al-Khamenei (RH) a gidansa da ke Abuja.
A yayin jawabinsa ga mahalarta, Jagora Sayyid Zakzaky ya bayyana yadda shahadar Sayyid Qa'id (RH) ta yi kamanceceniya da ta Imam Hussain (AS). Yace: “Tabbas shahadar Sayyid Qa'id ta fito da wadansu abubuwa shigen irin yadda Shahadar Imam Hussain (AS) wadda ta auku a Karbala ta bayyanar.”
Yace: “Imam Husaini (AS) ya sadaukar da ransa ne a Karbala don ya nuna ma al'umma ina gaskiya take, ina addini yake, kuma wane ne shugaba?” Ya kara da cewa: “Ba ma kawai al'umma ba, hatta ma bil'adama gabadaya ya san ina ne Adala take, ina kuma zalunci yake?”
Ya bayyana yadda aka tare Imam Hussain (AS) da sahabbansa da iyalansa a falalen daji, da nufin a kashe su a ji tsit, amma bayan kashe su ba a yi kwanaki 40 ba face makasansa sun tozarta, har Yazidu ya koma karbar duk sharadin da Imam Zainul Abidin (AS) ya bashi kafin komawarsu Madina.
Jagora yace: “Kun ga abinda suke tsammani dai ya zama ba haka ba ne, sadaukar Imam Hussain (AS) sai ta raya wannan addinin, aka san ina gaskiya take, aka gane waye azzalumi.”
Yace: “Shi Sayyid Khamenei (RH) ya san Shahada zai yi. Kuma dama dai Allah Ta'ala Ya jinkirta masa Shahadar ne. Tun shekara 1980 Miladiyya, aka saka masa b0m ya tashi da shi, aka kai shi asibiti ba numfashi, sai aka ga ya fara nunfashi, a nan ne ya rasa hannunsa na dama. Har zuwa shahadarsa da ya zo, hannunsa na dama baya aiki.
“Allah Ya jinkirta mashi shekara 46. Kun ga shi Shahidi ne. Don na san ko da muka je, wanda ko baku ji magana ba, za ku ga hoto, na san Malama Zeenah tace, tana roƙon shi ya roka mata Shahada. Sai yace, ai ke Shahidiya ce. Ya ce, ko yanzu dayanmu ya cika to Shahada ya yi. Shi ma Shahidi ne mai rai. Mu an mana harbin mutuwa ne, kuma Allah Ya raya mu, saboda haka, duk lokacin da mutuwa ta zo mana Shahada ce, an jinkirta mana shahadar ce izuwa lokacin da Allah Ya so.” Jagora ya bayyana.
Ya cigaba da cewa: “Muhimmin al'amari shi ne, shi fa ya san za a kashe shi ne, amma kuma ya tsaya akan cewa duk abinda zai samu mutanensa ya same shi. Wannan hatta wadanda suke tare da shi, sun san abinda zai same su (na Shahada), amma suka tsaya a tare da shi, tamaman, kamar yadda wasu suka tsaya tare da Imam Husaini (AS) suka ce sai dai su tafi tare, haka wadannan ma sun san abinda zai same su kenan. Kuma abinda ya same su, ya same sun.”
Yace: “Kashe wadannan mutanen, sai maƙiya suka dauka ai shikenan, sun gama da sama, da babban Jagora, da manya-manyan kwamandojin yaƙi duk an gama da su. Kwamandoji 40.
“Inda maƙiya suka buga, na farko sun dauka cewa al'amarin kwana hudu ne, farko su kawar da Jagora da manya-manyan Kwamandoji, jama'a kuma dama sun gaji da mulkin za su taso suce ba su so, shikenan kawai sai a sami sauyi hukuma. Kamar yadda suke cewa, za su je ne su ceci mutane daga ƙangin wannan hukumar. To amma tambaya, me yasa suka harbi yara ƙanana 'yan makarantar Firamare, 'yan shekara 6-12 a Minab kusan 200...?
“In wancan babban Jagora ne, to su wadannan yaran kashe su yana nufin mene? Su ma jagorori ne? Su ma kwamandoji ne na yaki?” Ya tambaya.
Yace: “Wannan zai gaya maka manufofin wadannan mutanen, al'umma suke son su kashe.”
Ya ba da labarin yadda suka kai hari makarantar yan mata na sakandire daga shekara 13 zuwa 18, inda suka kashe mutum 40 duk a ranar farko na harin. Yace, “to me yasa kuma kisan yan mata ne, 6-12 an kashe kusan 200, sannan 13-18 an kashe kusan 40. To shi mene ne ma'anar wannan?”
Ya ce, daga nan kuma Trump ya fara maganganu daban-daban. Yace zai share Iran a doron kasa. “Ha'a! Kai da kace ka je za ka ceci mutane, kuma yanzu za ka share su daga doron ƙasa? Meye ma'anar wannan? Ba ka ce za ka cece su ne saboda gwamnatin Musulunci ta ƙuntata musu ba? Ya za kuma ka share su a doron ƙasa?”
“Sai ya zo yace zai canza hukuma din. Zai harbi abubuwan more rayuwa da al'umma ke amfani da su, irin su ruwan famfo da wutan lantarki, da gajaje da hanyoyi, da sauransu, fi'ilan kuwa sai ya fara, sai ya fara harban masana'antu. To don Allah tunaninka masana'antan siminti ya shafi yaƙi? Aka harbi ruwan famfo, inda ake tace ruwan famfo ya zama ruwan sha... Kuma suka harbi wutan lantarki. To duk za ka tambaya, wai wannan ceton mutane ne wannan?
To sai gashi abin ya wuce nan. Wanda suke ce ma Sakataren Tsaro, muna iya cewa Ministan Tsaron Trump, yace, su a wurin su ba bambanci tsakanin Shi'a da Sunnah, duk Musulmi abokan gabansu ne, za su kashe duk cikansu ne, ko kuma a canza addinin. Wannan balo-balo ya fada, ba a asirce ba.”
Ya bayyana yadda hakan ya so ya farkar da kasashen Larabawa. Amma duk da haka, ya sake wata magana da suka ce ya sha giya ne a lokacin da ya yi ta. Inda yace "Kill all Muslims!" Inda ya bayyana yadda aka masa tambaya akan hakan a lokacin da giyar ta sake shi, amma ya yi dariya. Jagora: "Kuma har har yanzu maganar nan da ya yi na cewa ba ruwansu da bambanci tsakanin Shi'a da Sunnah, abokanan gabansu ne duka, za su kashe su duka ne, ko kuma a canza addinin. Shi mai gidansa bai ce abinda ya fada ba daidai ba ne.”
Yace, wadansu kasashen Larabawa sun yi tir da maganar. Kuma a can Amurka ma Musulmin can sun yi tir da maganar, haka ma wasu yan majalisar sun yi tir. Amma wasu sun ce, wannan mutumin abinda ya fada, hakikanin gaskiyarsa ne. “Dama abinda ba a fada ne, gaskiyar da ba a fada ne shi ya fada. Kun ga Shahadar Sayyid Khamenei ya tona mana wannan. Yanzu an gane su wane ne makiya, kuma me suke kiyayya da shi.”
Yace, har ila yau Shahadar Sayyid Khamenei ya nuna mana Munafukai. Wadanda suke fakewa da cewa suna kare wurare masu tsarki, ashe karnukansu ne. “Kuma ya nuna dama duk abinda Amerika ta saka a wadannan kasashe, ta sa ne don ta yaki Jamhuriyar Musulunci, domin kuma ta taimaka a kirkiri wannan Isra'ila babba.”
Jagora ya bayyana darussa daban-daban daga Shahadar Sayyid Qa'id (RH) da abubuwan da suka faru a kwana 40 din Shahadarsa, inda ya nuna cewa yanzu masu ganewa suna ganewa, marasa ganewa kuma ba mu sani ba.
Yace, Shahadar Sayyid Qa'id ya nuna, da ace wancan sarkin ne, mai suna Shah, da yake biye da su, da ba ruwansu da yakar Iran. Amma juyin Musulunci ne basu so. Yace: "Sun tambatsa shi, kuma in suna jin tsoro kar ya tambatsa a duniya, gashi ya tambatsa din, wadanda suke ƙiyayya sun dawo sun fasa. Da yawan mutane sun dawo sun daina kiyayya, kuma ido na ta budewa ne, ana ta ganewa, kuma an dinga ganewa kuma nan.”
Jagora ya kuma bayyana godiya ga Allah Ta'ala da ya sa Jamhuriyar Musulunci ta zama kakkarfan kasar da ta iya dakewa, ta ƙare addinin Musulunci da wannan al'ummar. Inda yace “Yakin da take yi tana yi ne ba domin kanta a matsayin ƙasa ba, domin al'umma ne gabadaya, da ma yantattun mutane gabadayansu. Duk masu neman Adala da yanci, to ta koya musu yanzu.”
Inda ya yi kira ga duniya ta tafi dare da su ne, maimakon su yi nasu daban, don ya zama in an taba su, zai zama an taba dukkansu ne.
Shaikh Zakzaky ya kuma jaddada alkawari da cewa: “Muna nan akan alkawari, muna ce ma Sayyid Qa'id, ka ba da jininka dominmu, kuma jininka bai tafi kawai ba. Arba'in din nan ya nuna mana irin tasirin da jininka ya yi, mun san kuma shekaru masu zuwa ma za su nuna, saboda haka, muna nan akan abinda ka ba da ranka a kai. Kuma ba za mu damu ba, tunda har kai ma ka ba da ranka, to ballanta mu? Mu ma a shirye muke mu hi tafarkinKa, ba ja baya. Muna nan a tafarkinka, har sai wannan addinin ya mallaki duniya bakidaya. Muna fatan Allah Ta'ala Ya gaggauta bayyanar Qa'im (AJ).”
A yayin zaman na jaje, Jagora (H) ya kuma jagoranci karanta Addu'ar Kumail, wanda ake yi a daren Juma'a, tare da sauran addu'o'in neman rahama ga Shahid Sayyid Qa'id (RH), da sauran Shuhada, da kuma neman kariyar Allah ga 'yan gwagwarmaya bakidaya.

Post a Comment