Labarai

Har yanzu akwai jan aiki a gaban mu duk da hukuncin Kotun Ƙoli- Atiku

 


Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya ce duk da cewa jam’iyyar ADC tsagin David Mark sun samu nasara a taƙaddamar shugabanci jiya a Kotun Ƙoli, a cewarsa har yanzu akwai jan aiki a gabansu, bai kamata su naɗe hannuwa su kwantar da hankalinsu ba. 

A cewar ya zama dole su sake tashi tsaye haiƙan domin ceto Najeriya, ta hanyar ƙwace mulki daga hannun shugaba Bola Tinubu. Jagoran ƴan adawar a Najeriya, ya ce wannan nasara ta ƴan ƙasar ce, jajirtattun miliyoyin mutane da suka ƙi amincewa da bada kai bori ya hau. 

A jiya Alhamis ne Kotun Ƙolin Najeriya ta yanke hukunci kan dambarwar shugabancin ADC, inda ta amince da tsagin David Mark, har ma ta bai wa INEC umarnin mayar da shi cikin jerin sunayen jagororin jam'iyyar a shafinta na intanet. To sai dai masana doka da na siyasa na ganin har yanzu tsuguno bata ƙare ba game da rikicin da jam'iyyar adawar ke fuskanta, ganin yadda kotu da ta yi hukunci a jiya, ta bayar da umarnin ci gaba da shari'ar a a kotun ƙasa. 

Ƙwararren lauyan Najeriya, Barista Abba Hikima ya ce har yanzu tana ƙasa tana dabo a rikicin ADC, domin a cewarsa Ƙotun Ƙolin har yanzu bata sare kan micijin ba, ganin yadda ta bada umarnin ci gaba da shari’ar a kotun ƙasa.

 A cewar sa, har gara ace kotun ba ta bawa ɓangaren David Mark kowace irin nasara ba, domin hakan zai basu damar fuskantar shugaba Tinubu a wasu jam’iyyun tun kafin lokaci ya ƙure. Su ma masana siyasa na ganin, wannan hukunci kamar shigo ba zurfi aka yi wa ƴan adawar, domin sanya su naɗe hannunsu tare da ci gaba da shirye-shiryen zaɓe a ADC, kuma daga bisani kotun ƙasa ka iya yanke hukuncin da bazai yi musu daɗi ba, a yanayin da lokaci ya ƙure musu. Ƴan adawar dai sun zargi gwamnatin Tinubu da ƙoƙarin murƙushe su, domin share hanyar sake komawar shi mulki, a dai-dai lokacin da ake tunkarar zaɓen shekarar 2027. 

Ko a baya-bayan nan, sai da masana siyasa suka ce Najeriya ta kama hanyar zama mai amfani da jam’iyya ɗaya tilo, ganin yadda dukkani manyan jam’iyyun adawa wato PDP da ADC, ke fama da rikicin cikin gida, wanda ake zargin Tinubu ne ya haddasa su saboda hana su taɓuka abun azo a gani a zaɓen da ke tafe.

Post a Comment

Previous Post Next Post