Ofishin Ƙaramar Ministar Harkokin Birnin Tarayya (FCT), Dakta Mariya Mahmoud, ya yi watsi da rahotannin da ke yawo cewa an gudanar da wasu naɗe-naɗe a muƙaman da ke ƙarƙashin ofishinta, yana mai bayyana cewa waɗannan ikirari ba su da tushe balle makama.
A cikin wata sanarwar musantawa da ofishin ya fitar, an bayyana cewa Mista Austine Elemue ne kaɗai mataimakin yaɗa labarai da aka naɗa a hukumance a ofishin Ƙaramar Ministar FCT, kuma shi ne kaɗai ke da ikon fitar da sanarwar hukuma ko yin magana a madadin Ministar, sai dai idan ta ba da wani umarni na musamman.
Sanarwar, wadda Elemue ya sanya wa hannu, ta kuma fayyace cewa Mista Bin Usman Rano ba ma'aikaci ba ne ko mataimaki a Ofishin Ƙaramar Ministar.
Ta ce ayyukan Rano suna da alaƙa ne da Dr. Mariya Support Group, wata ƙungiya da aka kafa domin tattara goyon bayan mata da matasa ga sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu da kuma wa'adi na biyu na Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, a zaɓen shekarar 2027.
Ofishin ya jaddada cewa duk wata naɗi, sanarwa ko izini da Rano ya bayar tana da alaƙa ne kawai da harkokin ƙungiyar goyon bayan, ba ta da wata alaƙa da Ofishin Ƙaramar Ministar Harkokin Birnin Tarayya, Hukumar Gudanarwar FCT (FCTA), ko Gwamnatin Tarayya.
Saboda haka, ofishin ya buƙaci al'umma, kafafen yaɗa labarai, hukumomin gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki da su yi watsi da duk wasu takardun naɗi, sanarwa ko ikirarin da ke nuna cewa sun fito daga Ofishin Ƙaramar Ministar.
A ƙarshe, ofishin ya sake jaddada aniyarsa ta ci gaba da gudanar da ayyukansa cikin gaskiya da riƙon amana, tare da bayyana cewa duk wata sanarwar hukuma za ta ci gaba da fitowa ne ta hanyoyin da aka amince da su da kuma ta hannun jami'an da aka ba wannan alhakin.

Post a Comment