Daga Wakilinmu
An bayyana alhini da jimami sakamakon rasuwar wata matashiya daliba, Zulaikhah Abdu Hameed Salihu Bomo, wadda ta rasu a shekarar 2026 bayan ta shafe kimanin shekaru hudu tana fama da rashin lafiya.
Marigayiyar an haife ta ne a shekarar 2007, inda ta taso cikin tarbiyya da neman ilimi tun daga matakin farko. Ta fara karatunta ne a makarantar firamare ta Staff School da ke Zariya, inda ta kammala a shekarar 2020.
Bayan haka, ta ci gaba da karamar sakandare a makarantar God’s Time da ke Hayin Dogo, Samaru, inda ta samu nasarar kammalawa kafin ta zarce zuwa babbar sakandare a makarantar guda, wadda ita ma ta kammala cikin nasara. Ta kuma rubuta jarabawar kammala sakandare ta NECO.
A bangaren ilimin addini kuwa, marigayiyar ta shiga makarantar Haddar Alkur’ani a shekarar 2019, inda ta yi karatu har zuwa bana, kuma ta kammala haddar kafin shirye-shiryen walimarta. Sai dai kafin a gudanar da walimar, Allah Ya yi mata rasuwa a makarantar Babul’ilmi Academy.
Rahotanni sun nuna cewa Zulaikhah ta yi fama da rashin lafiya na tsawon shekaru hudu, amma duk da haka ta ci gaba da kokarin neman ilimi da jajircewa har zuwa karshen rayuwarta.
Rasuwarta ta girgiza iyalai, abokai da malaman da suka san ta, inda da dama suka bayyana ta a matsayin daliba mai ladabi, hakuri da jajircewa.
Allah Ya jikanta da rahama, Ya gafarta mata kura-kuranta, Ya sanya Aljannatul Firdausi ta zama makomarta.

Post a Comment