Matar jagoran Harkar Musulunci ƙarƙashin jagorancin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), Malama Zeenatuddeen Ibraheem, ta yi kira ga Musulmi da Kiristoci a faɗin duniya da su haɗa kai wajen yaƙi da zalunci domin tabbatar da adalci da inganta rayuwar al’umma.
Ta bayyana hakan ne a wajen rufe taron ƙasa da ƙasa karo na biyar kan fikirar Musulunci mai taken “Halin da ake ciki: ina mafita”, wanda Dandalin Ɗalibai da Malamai tare da haɗin gwiwar Dandalin ƴan’uwa mata suka shirya a Bauchi.
Taron wanda ya ɗauki kwanaki huɗu, ya samu halartar mahalarta daga Najeriya, Nijar, Chadi da sauran ƙasashen Afirka.
A jawabinta, Malama Zeenatuddeen ta jaddada muhimmancin bin koyarwar Alƙur’ani da Sunnah a rayuwar Musulmi, tana mai cewa wajibi ne ga mabiya addinin Musulunci su rayu bisa koyarwar Allah da ManzonSa.
Ta ce manufar taron ita ce tunatar da Musulmi alhakin da ke kansu na zama nagartattun mabiya addini, tare da jaddada cewa ba wai ana tilasta wa kowa ya zama Musulmi ba ne, amma dole ne a guji rayuwa saɓanin koyarwar addini.
Dangane da rikice-rikicen duniya, musamman wanda ya shafi Amurka da Isra’ila kan Iran, ta bayyana lamarin a matsayin gwagwarmaya tsakanin masu zalunci da waɗanda ake zalunta, tana mai jaddada goyon bayanta ga ɓangaren masu tsayin daka kan zalunci.
Ta ƙara da cewa ba za a samu zaman lafiya mai ɗorewa ba a duniya matuƙar ana yin shiru kan zalunci, tana mai cewa dukkan Annabawan Allah sun zo ne domin yaƙi da zalunci da tabbatar da adalci.
Hakazalika, Malama Zeenatuddeen ta bayyana cewa taron na da nufin ƙarfafa fahimta kan manufofin Harkar Musulunci tare da ƙarfafa tsayin daka kan zalunci a duniya baki ɗaya, musamman goyon bayan al’ummar Falasdinu.
Ta kuma gargadi ‘yan Najeriya da su yi hattara da tasirin ƙasashen waje, tana mai cewa wajibi ne a kare ‘yancin kai na ƙasa.
A nata ɓangaren, Dr. Fatima Ismail daga Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya, ta ce an tsara taron ne domin wayar da kai kan adalci da ƙarfafa tsayin daka kan zalunci a duniya, tare da kira ga haɗin kan Musulmi da Kiristoci.
Bayan kammala taron, dubban mahalarta da mabiya Harkar Musulunci sun gudanar da zanga-zangar lumana a Bauchi, inda suka yi tattaki zuwa zagayen Bankin CBN suna bayyana goyon bayansu ga Falasdinu tare da yin Allah wadai da manufofin Amurka da Isra’ila.
Da yake jawabi yayin gangamin, Injiniya Abdullahi Musa ya jaddada cewa yaƙi da zalunci wajibi ne ga dukkan mabiya addinai, yana mai cewa gwagwarmaya don adalci ita ce manufar dukkan Annabawa.
Shi ma wakilin ƴan uwa musulmi Almajiran Shaikh Zakzaky a Gombe, Sheikh Muhammad Abbare, ya buƙaci shugabannin siyasa a Najeriya da su mayar da hankali wajen kawo ƙarshen kashe-kashe da zalunci, maimakon tsunduma cikin shirye-shiryen zaɓe tun da wuri, yana mai jaddada cewa adalci shi ne ginshiƙin shugabanci nagari.
.jpg)
Post a Comment