Araqhchi ya ƙaryata Amurka kan asarar da ta yi a yaƙinta da Iran

 


Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqhchi ya ce ma'aikatar tsaron Amurka ta yi ''ƙarya'' kan asarar da ƙasar ta tafka a yaƙin Iran. Tun da farko sakataren tsaron Amurka, Pete Hegesett ya bayyana a gaban kwamitin ayyukan soji na majalisar dokkin Amurka cewa ƙasarsa ta yi asarar dala biliyan 25 a yaƙin Iran. 

To sai dai cikin wani saƙo da Araqhchi ya wallafa a shafinsa na X, ya ce ''ma'aikatar Pentagon ta yi ƙarya. Cacar Netanyahu ta janyo wa Amurka asarar dala biliyan 100 zuwa yanzu, wato ninki huɗun abin da suka bayyana''. 

Mista Araqhchi ya ƙara da cewa harajin da Amurkawa ke biya ya ƙaru, abinda magidanta ke kashewa a wata, yanzu ya kai dala 500, kuma ƙaruwa yake yi cikin sauri''. Ministan wajen na Iran ya ce abin da tsarin nan na ''Isra'ila a farko'' ke nufi shi ne ''Amurka a ƙarshe''. 

Tun da farko, sakataren tsaron Pete Hegsett ya kare ƙoƙarin ma'aikatar tsaron ƙasar a yaƙin Iran a gaban kwamitin aikin soji na majalisar wakilan Amurka. Inda ya ce kwalliya ta biya kuɗin sabulu, tun da an ''hana Iran mallakar makamin nukiliya''.

Post a Comment

Previous Post Next Post