Mu’utamar na Muballighun Yana Gudana a Abuja

 


A ranar Alhamis 12 ga watan Zulƙada 1447 daidai da 30 ga watan Afrilun 2026, aka buɗe zaman Mu’utamar na Lajnar Tarbiyya wa at-Tableeg na ƙasa da ƙasa a Abuja.

Taron ya samu halartar ‘yan’uwa musulmi Almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) maza da mata daga sassa daban-daban na ƙasar nan, har ma da cikin birnin Abuja.

Manyan masana a fannoni daban-daban na ilimi ne za su gabatar da darussa iri-iri a muhallin taron da ke Markaz Karmajiji, wanda zai gudana na tsawon kwanaki huɗu, in shā Allah.

Post a Comment

Previous Post Next Post