Daliban Jami’atul Al-Mustapha Sun Yi Bikin Yaye Daliban ISMA Karo na Biyu


 Daga Mubaraka Adam Tsafe

Daliban makarantar Jami’atul Al-Mustapha Niger masu alaka da tafarkin Sayyid Ibrahim Zakzaky (H) sun gudanar da bikin yaye daliban makarantar ISMA karo na biyu.

Bikin ya gudana ne a ranar Lahadi, 12 ga Afrilu, 2026, a makarantar ISMA (Y. Ahmad Health Care Training Center), wadda wasu dalibai suka assasa domin taimakawa ‘yan’uwansu wajen koyon harkokin kiwon lafiya.

An fara shirin da misalin karfe 11:00 na safe, inda aka bude da addu’a da karatun Al-Qur’ani mai girma. Daga nan sai aka gayyato Shaikh Muhammad Ahmad (BBC), wanda ya gabatar da muhimmin jawabi mai taken “Amfanin Ma’aikatan Lafiya ga Al’umma.”

Bayan kammala jawabin, wasu daga cikin daliban makarantar sun gabatar da takardun bincike (paper presentation) kan muhimman batutuwa kamar “Waye First Aider?” da kuma “Hepatitis B.” Haka kuma an gudanar da gasar tambayoyi da amsoshi (quiz), wadda ta kara kayatar da taron.

Abu mai daukar hankali a wajen bikin shi ne yadda aka gudanar da shirin cikin harsuna hudu, wato Turanci, Faransanci, Larabci da Hausa, domin fadada fahimta ga mahalarta.

A yayin bikin, an ba mahalarta damar gabatar da kyaututtuka ga daliban da suka kammala karatunsu, inda abokan karatu da ‘yan’uwa suka nuna farin ciki ta hanyar ba su kyaututtuka.

Haka zalika, daliban da suka kammala karatun su ma sun nuna godiya ga malamansu ta hanyar ba su kyaututtuka. Har ila yau, jami’ar Jami’atul Al-Mustapha ta samu kyauta a matsayin nuna jin dadi da yabawa ga gudunmawar malamanta wajen cigaban wannan shiri.

Bikin ya gudana cikin nasara da farin ciki, tare da jaddada muhimmancin ilimin kiwon lafiya a tsakanin al’umma.

Post a Comment

Previous Post Next Post