Dandalin Ɗalibai Na Harkar Musulunci Ta Shirya Taron Bita A Katsina

 


Daga Ahmad Basiru

Dandalin ɗalibai da Malamai na Harkar Musulunci ƙarƙarshin jagorancin Sheikh Ibraheem Zakzaky (H), a garin Katsina sun shirya taron bita karo na shida kamar yadda suka saba gabatarwa.

An buɗe taron da addu’a, a ka yi karatun Alƙur’ani mai girma. Mai kula da ayyukan dandalin a yankin Katsina ne ya yi jawabin maraba da baƙi a wajen.

An gabatar da jawabai da dama a wajen na farko ya yi jawabi mai taken ‘Cyber Warfare and the Student Community: Risks and Responsibilities’ wanda Dr. Abdullahi Isa ya gabatar. Ya ce; “Duniya ta zama ‘Digital world’, wato komai ya dawo kan Intanet”

Mai jawabi na gaba, Dr. Abdullahi Yar’Adua ya yi nasa jawabin ne kan  ‘The Genesis of the Islamic Movement’ cikin jawabin ya bayya yanda su Sheikh Zakzaky suka fara ƙira, har zuwa lokacin da ƙiran ya iso garemu.

An kuma gabatar da Symposium mai taken ‘From representation to impact: Reviving campus life through strong’

Academic forum.’ Wakilai huɗu na Makarantun dake faɗin Jihar Katsina ne suka gabatar, sun haɗa da FUDMA, UMYU da sauransu. Sun yi doguwar tattaunawa a kan ƙalubalen da Academic Forum ke fuskanta da hanyoyin da za’a bi wajen magancesu.

A ƙarshe, an rufe da jawabin Engr. Hamisu B. Imam; ya yi jawabin rufewa tare da rufewa da addu’a.

Dandalin yaɗa labarai na Harkar Musulunci.

Post a Comment

Previous Post Next Post