Dandalin Yada Labarai (Media Forum) na Harkar Musulunci ya sanya tashar ABS Channel a babban shafin Hausa na Harkar Musulunci da ke www.harkarmusulunci.ng
Masu ziyartar shafin za su iya shiga kai tsaye, inda za su ga wani sashi (column) mai taken “ABS Channel Live”. Da zarar an danna wannan sashi, za a buÉ—e gidan talabijin É—in kai tsaye daga tauraron dan adam, wanda zai ci gaba da watsawa na tsawon awanni 24 domin masu kallo su ci gaba da samun damar kallon shirye-shirye cikin sauÆ™i.
An yi wannan tsari ne domin sauƙaƙa hanyoyin shiga da kuma tabbatar da cewa masu ziyara ba za su wahalar da kansu wajen neman tashar ba, tare da ba su damar samun dama kai tsaye ba tare da mantawa da inda za su shiga ba.
-Media Forum Na Harkar Musulunci a karkashin jagorancin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H)
27/2/2026

Post a Comment