Daga Ofishin Sayyid Ibraheem Zakzaky (H)
Da yake jaddada isar da ta'aziyyarsa
na Shahadar Sayyidul Qa'id (RH), a ranar Litinin 13 ga Ramadan 1447 (2/3/2026),
Jagoran Harka Islamiyya, Sayyid Ibraheem Zakzaky (H), ya bayyana irin yadda aka
girgiza al'umma da dauke babban rukuninta a daidai wannan lokaci.
“Daidai wannan lokaci mawuyaci, an
girgiza mu da rashin babban rukuni na wannan al'umma, Sayyid Qa'id (RH), wanda
Shahadarsa ta kasance a ranar Asabar din nan. Ko shakka babu mun girgiza.” Inji
Jagora Sayyid Zakzaky (H).
Jagoran ya miƙa ta'aziyyarsa Limamin
wannan zamani namu, Sahibul Asr Imam Mahdi Arwahuna lahu fidah, dangane da
rashin wannan rukuni nasa. Sannan ya kara isar da ta'aziyya ga Maraji'anmu na
addini masu girma, da jagorori da kwamandojin yaƙ| na Jamhur|yar Musulunc|, da ɗaukacin
al'ummar |ran, da al'ummar Musulmin duniya, da ma dukkanin ʼYantattu a duk
duniya bakidaya, dangane da wannan rashi. “Wannan rashi ne gare mu gabadaya
wanda duk cikanmu muka yi. Kuma abu ne da ya shafe mu gabadaya.” Ya jaddada.
Sayyid Zakzaky ya bayyana yadda
Allah Ta'ala Ya ma Ayatullahil Uzma Sayyid Aliyul-Khamene| (RH) taufiƙi na yin
hidima ga addini tun yana matashi har zuwa tsufansa. Yace yana cikin manyan
almajiran Imam Al-Khomaini (QS) tun yana matashi, kuma da su aka yi wadannan
gwagwarmaya na tabbatan add|nin Musulunci a |ran har juyin ya samu, shekara 47
da suka wuce.
Ya bayyana yadda makiya suka yi ta
kokarin ka`she mutanen da suke rukunai na juyin tun farko, wanda maƙiya suka k`she
Ayatullah Mutahari, da Ayatullah Bahishti, da shugaban ƙasa Ali Raja'i. Yace,
“shi ma Sayyid Ali Khamene`| sun so su ka`she shi tun shekara 46 da suka wuce,
inda bom ya tashi da shi, har aka ɗauka ma ya yi shahada, amma bayan kai shi
asibiti aka ga yana numfashi. Kuma ya farfado daga baya, wannan ya yi
sanadiyyar rashin aikin hannunsa na dama, Allah Ta'ala dai Ya raya shi.”
Ya kara da cewa: “Kuma bayan shekara
guda da wannan harin, bayan Shahadar Ali Raja'i, shi (Sayyid Qa'id) aka zaɓa
shugaban ƙasa. Ya shekara takwas yana shugaban kasan. Kuma shekara goma cur
bayan juyi din Imam Al-Khomaini (QS) wafatinsa ya kasance, sai kuma ya zama zaɓi
ya faɗa kan shi Sayyid Ali Khamene`| a matsayin shi ne magajin Imam Khomaini,
yau shekara 37 cur yana riƙe da wannan matsayi.”
Jagora ya bayyana yadda Shaheed
Sayyid Qa'id (RH) ya tsaya ƙyam a manhajan Imam (QS) kai kace Imam Khomaini din
ne ke da rai. Yace: “Ya tsaya da wannan matsayi na Jagorancin wannan al'umma,
da hikima, da hangen nesa, da dauriya, har ya zama abubuwa suka zauna yadda
suka dace.”
Ya kuma bayyana yadda Shaheed Sayyid
Qa'id (RH) ya ƙirƙiro wasu abubuwan da suka taimaka wajen samar da haɗin kan
al'ummar Musulmin duniya, da kuma kyakkyawan alaƙa da dukkanin mutane, kamar
kirkiran “Majma'ul Alamiy lit-Taqrib bainal Mazahibul Islamiyya”, da “Majma
Ahlulbait al-Alamiy”, da kuma “Sahwatul Islamiyyah”, da “Mu'utamarul Adyan”
Wanda ake kusanto da addinai,, da sauransu. Yace, “(Sayyid Qa'id (H) ya
jagoranci gwagwarmaya ne na kwatan al'umma gabadayanta, don haka ne ma wadansu
kasashe an tafi da su a wannan gwagwarmaya din.”
Ya bayyana yadda Shaheed Sayyid
Khamene`| (RH) ya tsaya ƙyam domin baiwa al'ummarsa kariya, a yayin da aka nemi
ya bar gidan da yake tunda an san da shirin makiya na kawo masa hari, amma ya nuna
ba zai gudu inda zai tsira ya bar al'ummarsa a halaka su ba.
Yace: “Wadannan mutanen (masu kisan
kai) suna tutiyar cewa, wai leken asirinsu ne ya gano inda [Sayyid Khamene`|]
yake. To, ai ba wani wuri yake ba, gidansa ne. A gidan da yake kwana a nan aka
kashe shi, shi da matarsa, kuma aka kashe 'yarsa da mijinta, da jikanyarshi,
yarinya mai suna Zahra 'yar wata hudu da haihuwa. Ba inda suka je. Nan ya
zauna. Nan kuma abin ya same shi, kamar yadda ya samu kowa.
“Yadda mutanen nan suka kai
hare-hare, ba su gushe ba suna ka`she kowa, shi sai yana ganin to don me zai je
ya buya a wani wuri ya samu mafaka? [Ya zabi ya zauna] abinda yake samun
al'ummarsa shi ma ya same shi. Wannan kuma irin matsayar da shi ma Imam
Khomaini (QS) ya ɗauka kenan, lokacin da ana tunanin ko za a kai shi wani wuri
ne? Yace to, waɗannan mutanen da suke makwaftaka da shi fa, in aka ka`she su
fa? Sai dai [ya zauna a cikinsu] a kashe su tare.” Jagora ya fada.
Ya cigaba da cewa: “Allah Ta'ala Ya
kiyaye Imam (QS) har wafatinsa ya zo. Shi kuma Sayyid Khamene| Allah Ta'ala Ya
ga daman ya karrama shi da shahada a karshen rayuwarsa, ya zama ba rashin
lafiya ya yi aka kwantar da shi a asibiti har ya cika ba.”
Ya kara da cewa: “Ko da ma rashin
lafiya ya yi, aka kwantar da shi a asibiti, ya cika, to Shahada ya yi, don dama
Shahidi ne mai rai. Shekara 46 yana fama da abinda yake fama da shi na rashin
hannu guda. Da Allah Ya so da tun wancan shekarar da ya yi Shahada. Amma Allah
Ta'ala Ya kare shi [har zuwa wannan lokacin].
Harwayau, Jagora (H) ya bayyana
yadda aka riƙa yunkurin ka`she Sayyid Khamene| a lokuta daban-daban, Allah
Ta'ala na kare shi, har zuwa yanzu da lokacinsa ya yi, ya tafi a irin tafarkin
kakansa Amirulmumin (AS) wanda shi ma a irin wannan wata na Ramadan aka
Shahadantar da shi.
Yace, bayan mun yi bakin ciki da
takaicin an raba mu da Jagora, a lokaci guda mun san cewa lokaci ne ya yi na
tafiyansa, kuma Allah Ta'ala Ya so ya zama karshe Shahada ne. Ya kuma so ya
hutar da shi hutun har abada Insha Allah, yazuwa rahamar Ubangijinsa.
Da yake magana da masu ki`san,
Jagora (H) ya bayyana abinda suka yi a matsayin ragwanci da tsoro. “Kun nuna ku
ragwage ne matsorata da baku iya komai ba sai kisan kai.”
Yace: “Yaƙi ana yi ne tsakanin
mayaƙa, ba ana zuwa ne gidan mutum a ka`she shi tare da iyalinsa ba. Ku kuwa
abinda kuka iya kenan. Ku ka`she yara, ku ka`she tsofaffi da kowa da kowa, ku
ce kuna yaki. Ku barna kuke yi. Ku mabarnata ne, kuma barnar kuke dauka a
matsayin yaƙi.”
Ya bayyana manufar su shi ne
durkushe Jamhuriyar Musulunc| don kar addini ya fadada, da kuma yunkurin samun
damar mamaye kasashen Musulmi ciki har da garin Makkah da Madina ta hanyar
amfani da abinda ya kira 'cancer' (HƘI) a Gabas ta Tsakiya. Yace: “Wannan
abinda wadannan mutane suka yi, Insha Allahu zai zama sharri gare su, alheri
gare mu.”
Yace, “Kun tabbatar in Jamhuriyar
Musulunc| na nan, addini zai cigaba da dagowa. To kun yi kuskure, domin wannan
abinda kuka yi, ya nuna kun kawo karshenku ne. Insha Allahul Azeem, jinin
Sayyid Qa'id, zai farauce ku har zuwa ƙarshe. Kuma Insha Allahu, suqudinku
kamar ya zo, kun ruguje kenan Insha Allahul Azeem. Sahayonanci da Amer|kanci,
da danniyan Amer|kawa Insha Allah ya kawo karshe kenan. Kun yi barnan da ba za
ku yi mana wani fiye da shi ba. Kun yi na karshe Insha Allahul Azeem.”
A karshe, Jagora Shaikh Ibraheem
Zakzaky (H) ya yi kira ga al'ummar Musulmin duniya da su fahimci inda aka sa
gaba, kuma mu fahimci cewa addininmu da mutuncinmu da komai namu ne makiya ke
kokarin su rusa.
Yace: “Insha Allahul Azeem wannan
karo ne tsakanin 'haq' da 'baɗil', kuma kamar yadda Allah Ta'ala Ya alkawarta
mana 'innal baɗila kana zahuqa.` Ba da jimawa ba, Allah Ta'ala zai daukaka
wannan al'umma, Ya tabbatar da ita ba da jimawa ba. Muna rokon Allah Ta'ala Ya
gaggauta bayyana wanda da bayyanarsa ne za a samu mafita.”
Da misalin karfe 9:00 na daren yau
Litini, za a saka cikakken Jawabin Ta'aziyyar na Jagora (H) a tashar Satellite
na ABS TV da ke wannan adireshin: Eutelsat 16est/Amos17 Frequency
12169/H/30000.
Ga waɗanda ke amfani da waya kuma za
su iya kallo ta wannan link ɗin:
https://playtv4k.live/live/ABS/index.m3u8
@Szakzakyoffice
#Alfatiha
#FreePalestine
#PrayForPalestine
#RamadanMubarak
#WeStandWithIran
#OurMartyrsOurHeroes
02/03/2026
Post a Comment