Dakarun kare juyin juya halin musulunci a nan Iran wato IRGC ya bada sanarwan cewa sai ya dauki fansar kissan da gwamnatin Amurka ta yiwa Janar Shahid Qasen Sulaimani, tare da cewa shekaru 6 da shahadarsa, tunaninsa da aikin da ya bari na tafiya a cikin dakarun da ya tarbiyantar a yankin Asia ta kudu.
Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto bayanin da dakarun suka fitar a safiyar yau Asabar yana cewa, koma bayan da gwamnatin kasar Amurka take fuskanta a ayyukan sojenta ayankin da kuma duniya yana daga cikin tasirin ayyukan Janar Sulaimani da makarantarsa. Labarin ya kara da cewa shugaban kasar Amurka Donal Trump da kuma mashayin jinin mutanen yankin Asiya Benyamin Natanyahu sun bayyana gazawarsu a lokacinda suka kashe Janar Sulaimani a lokacinda ya sami nasar wargaza shirye shiryensu a yankin.
Sun ce dakaru masu gwagwarmaya a yankin zasu dauki fansar kissan sa a lokacinda ya dace, kan wadanda suke da hannu a cikin kashe shi.

Post a Comment