An buɗe ginin Sayyidah Fatimah al-Zahra (AS) a birnin Najaf mai tsarki da ke Jamhuriyar Iraki, a kusa da haramin Amirul Muminin, Imam Ali ibn Abi Talib (AS), tare da halartar wakilai da baƙi daga ƙasashe daban-daban na duniya. An kuma haɗa bikin buɗe ginin da bikin tunawa da ranar haihuwar Sayyidah Fatimah al-Zahra (AS).
An gudanar da taron ne a wani yanayi mai cike da ruhi, tsarki da girmamawa, a ƙarƙashin inuwar haramin Amirul Muminin (AS), a birnin Najaf al-Ashraf mai albarka.An kammala wannan katafaren gini mai albarka ne da kyawawan abubuwan fasahar gine-gine na zamani, tare da gudummawar ƙwararrun masu sana’a, waɗanda suka ƙera wani babban aiki da ya haɗa sahihancin fasahar Musulunci da ruhin zamani. Ginin ya zama shaida ga haɗuwar imani da ƙwarewa, da hidima da kyawawan dabi’u.An gudanar da bikin buɗe ginin ne a gaban Babban Malamin Musulunci, Sheikh Mohammad Mohammadi, Shugaban Ofishin Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci, Imam Sayyid Ali Khamenei (H).
Haka kuma, an samu halartar Babban Malami Ayatollah Sheikh Hassan al-Jawahiri, tare da jami’ai daga Haramin Imam Ali (AS), malamai, manyan mutane da masu hidima.A yayin taron, mahalarta sun ɗaga hannuwansu sama domin yin addu’a, suna gode wa Allah Maɗaukakin Sarki bisa nasarar kammala wannan muhimmin gini mai albarka.
Wannan katafaren gini ba wai faɗaɗa birni kawai ba ne, wuri ne na ibada, ilimi da hidima, tare da zama fitila wajen koyar da bin halaye da koyarwar Shugabar Matan Duniya, Sayyidah Fatimah al-Zahra (AS). Haka kuma, za a rika sauke baƙi kyauta ga masu zuwa ziyarar Amirul Muminin (AS).Ta haka ne Najaf al-Ashraf ke ci gaba da kasancewa cibiyar imani, da wuri mai haɗa zukatan bayin Allah masu ƙaunar gaskiya, adalci da aminci.

Post a Comment