Daga Hussaini Yero
’Yan’uwa Musulmi, almajiran Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) na yankin Funtua, sun gudanar da taron Mu’utamar Masu Mas’uliya domin ƙara fahimtar juna da kuma tattauna ayyukan da suka rataya a wuyan masu tafiyar da bangarori daban-daban na Harkar Musulunci (Mas’ulai). An gudanar da taron ne a ranar Lahadi 25 ga watan Janairun 2026 a garin Funtua ta jihar Katsina.
A wajen taron, Farfesa Isah Haruna Mshelgaru ya gabatar da kasida mai taken “Mas’uliya Amana Ce a Musulunci.” A cikin kasidar, Farfesa Mshelgaru ya bayyana cewa mas’uliya amana ce da aka ɗora wa ɗan’uwa da aka ba alhakin tafiyar da wani bangare a Harka. Ya jaddada cewa wajibi ne duk wanda aka ba mas’uliya ya fahimci nauyin da ke kansa, tare da bincike da koyo idan bai da isasshiyar masaniya kan aikin da aka ba shi, domin ya sauke amanar da aka ɗora masa yadda ya dace.
Farfesan ya ƙara da cewa duk wani aiki da ɗan’uwa zai yi a cikin Harka, dole ne ya yi shi domin Allah, domin yin aiki saboda Allah ne kawai zai taimaka wa mutum wajen cika mas’uliyarsa yadda ya kamata.
Har ila yau, ya bayar da misali kan bangaren malamai (Fodiya), inda ya ce suna da alhakin samar da ɗaliban da Harka ke buƙata tun daga matakin firamare har zuwa sakandare, a bangaren ilimin addini da na boko. Idan ba su iya cika wannan nauyi ba, ya dace su sauka domin a bai wa waɗanda za su iya cika aikin damar jagoranci. Haka nan ya ce a kowane bangare na Harka, idan jagora ya kasa samar da abin da Harka ke buƙata, ya kamata ya miƙa ragamar aiki ga wanda ya fi dacewa.
A nasa jawabin, Malam Kabir Imam Malunfashi ya yi bayani kan siffofin Mas’ulai da ayyukansu a Harkar Musulunci. Ya bayyana cewa babbar siffar Mas’uli ita ce kyawawan ɗabi’u, tare da guje wa munanan halaye da za su iya jawo wa Harka zargi ko batanci. Ya kuma jaddada muhimmancin haƙuri, domin masu mas’uliya za su fuskanci jarabawa a yayin gudanar da ayyukansu.
Malam Kabir Imam ya kuma bayyana cewa bangarorin Harka suna da alaƙa kai tsaye da Jagora wajen tafiyar da ayyukansu, don haka ba lallai ba ne su rika neman izinin Wakilin ’Yan’uwa na gari a kowane lokaci, muddin suna aiki bisa tsarin da Jagora ya shimfiɗa. Ya ƙara da cewa masu mas’uliyar shirya taruka suna aiki ne bisa umarnin Jagora, kuma duk abin da suke yi yana cikin iyakar izini da jagorancin sa.
Ya jaddada cewa duk wani aiki da masu mas’uliya za su yi, dole ne su yi shi domin Allah, kamar yadda Jagora ke yawan jaddadawa, domin babu mai yin aiki saboda Allah face mumini na gaskiya.
A ɓangaren shawarwari, Alhaji Ali Khalil ya ja hankalin Mas’ulai da ’yan’uwa da cewa ba a ba mutum jagoranci domin ya yi mulkin kai tsaye ba, sai domin a yi aiki tare don samun nasarar Harka. Ya kuma shawarci Wakilan ’Yan’uwa da su rika bibiyar ayyukan bangarorin Harka, su rika ba da shawarwari da ƙarfafawa, domin hakan ne zai taimaka wajen bunƙasar Harka.
Haka kuma, an shawarci ’yan’uwa da su rika halartar tarurrukan Harka a Abuja yadda ya kamata, ba tare da tauye wakilcin garuruwansu ba.
A jawabin rufewa, Malam Rabiu Abdullahi Funtua ya bayyana cewa duk wanda ya yi sakaci ko ganganci a kan mas’uliyar da aka ba shi, har ya jawo cikas ga Harka, to ya saba wa Allah kuma ya yi zagon ƙasa ga tafiyar Imamul Hujja (AJ). Ya kuma jaddada cewa Jagora ya sha bayyana a jawabansa cewa addini zai tabbata, don haka wajibi ne kowa ya bayar da gudunmawarsa gwargwadon iyawarsa domin tabbatar da addini karkashin jagorancin Sheikh Ibraheem Zakzaky (H).
A ƙarshe, Malam Rabiu Abdullahi ya yi kira ga ’yan’uwa da cewa idan Wakilin ’Yan’uwa na gari ya aikata kuskure, a bi hanyar maslaha wajen gyara shi ta hanyar nasiha da ladabi, ba ta hanyar faɗa ko cin mutunci ba.

Post a Comment