Daga Ofishin Jagora Sayyid Ibraheem Zakzaky (H)
A ranar Asabar, 28 ga Rajab 1447 (daidai da 17/1/2026), Harkar Musulunci, karkashin Jagorancin Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) ta gudanar da taron tunawa da Shahidai (Yaumus Shuhada) karo na 35 a garin Abuja.
Da yake jawabi a wajen taron, Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya jaddada alkawari ga Shahidan Harkar Muslunci akan cewa, muna nan akan abinda suka bayar da jinainansu akansa. Yace: “Muna nan akai daram. Insha Allahul Azeem za mu tabbatar da cewa jinainanku ba su tafi a kawai ba. Muna nan ko nasara, ko kuma har mu cimmuku. Bare ma da nasarar, da cimmukun insha Allah duk za mu samu.”
Ya kara da cewa: “Insha Allah muna nan daram akan wannan hanyar. Kuma wanda duk ke sa rai, ya ma fid da rai, amma idan barazanar kisa ne, sai mu ce, ya ba da kokari, mu ba za a taba tsoro da wannan ba. Kuma lallai insha Allahul Azeem, nasara kamar ta zo, kuma ta ma kusa. Masu ganin abin ba zai yiwu ba, su fi da rai, wannan alkawari ne na Allah, kuma Allah ba ya saba alkawarinsa, addinin nan insha Allahul azeem, kamar ma ya dawo ya kafu daram-dam! Insha Allah.”
Shaikh Zakzaky yace: “Mahukunta suna so su za a bi, duk wanda aka ce shi ne shugaba, to shi yana son shi za a bi (kawai), ba ya son ya ga wani yana da tasiri, lasiman wanda ya tsaya a tafarkin Allah kyam.”
Yace: “Yana iya samun wanda ke ja da shi a sarautansa don shi ma ya gaji sarautan su yi fada, amma ka ga wanda yake magana dangane da sha’anin addini, to shi abin tsoro ne (a wajensa), don shi yana neman ne ya koma da mutane tafarkin Allah Ta’ala. Shi ne kuma abinda mahukunta suka ki.
“Shi yasa muka ce, lallai shahadar Imam Kazeem (AS) ya zama ramzi, na cewa, shi Shahidi ba wani laifi yake yi ma masu kashe shin ba, illa yana cewa Ubangijinsa Allah ne. In ya tsaya yace Ubangijinsa Allah ne, ya tsaya kyam to ya yi babban laifi a wajen mahukunta. Domin su mahukunta abinda suke so shi ne, ya daina cewa Allah za a bi shi kadai, ya hada har da su.” Inji Jagora.
Yace: “Shi wanda aka kashe shi saboda Allah, an masa yanke ne, maimakon ya bi hanya mai tsawo ya je Aljanna, sai aka ce, wuce kawai. Wannan ba karamin rabauta ba ne.”
Ya kara da cewa: “Su (Shuhada) ba suna cikin damuwa ba ne, suna cikin farin ciki ne, mu ne abin ji. Kamar yadda nassin Alkur’ani, Allah Ta’ala yake bayar da labari a Ayar ‘Yastabshiruna…’”
Yace, su kuwa azzalumai suna ganin suna kokari ne ta hanyar aukar da Shahada, domin su hana tabbatan addini. “Shi kuma wannan (takurawa da kisan da suke yi) bai taba hana aukuwar al’amari ba.”
Jafora ya bayyana cewa, wanda duk ya san cewa in an kashe shi zai koma ga rahamar Allah Ta’ala ne, to shi ba za a taba bashi tsoro da mutuwa ba. Yace: “Kamar ka ce masa ne, in ka kuskura ka yi min kaza, sai in kai ka Aljanna kasha shagali.” Don haka yace, zai kara kaimi ne.
Shaikh Zakzaky ya bayyana yadda azzalumai ke ganin suna da karfin kotu da kurkuku, da kuma kisa da bindiga, inda yace: “To amma Allah Ta’ala Yana da Zabaniyawa, Yana kuma da Saqar, da Sa’ir, da Jaheem, da Hawiya, da Laza, da Huddama. Duk yana da su, Yana iya saka mutum a duk inda Ya ga dama, in ya yi masa laifi.”
Yace, kenan mutum zai ga cewa, in ya dake a tafarkin Allah Ta’ala, to zai ci riba biyu ne, su kuma wadanda suke kokarin fada da shi, hasara biyu ne; na farko ba za su yi nasarar hana tabbatan abinda basu so ba, kuma za su hadu da azaba mai radadi a Lahira ranar Kiyama.
Yace: “Abinda suke so shi ne su kawar da addini, shi kuma addinin wannan sadaukarwar ne yake tabbatar da shi.” Ya kara da cewa: “Da sun sani, da ma sun kyale. Amma ba za su taba kyalewa ba. In ka ga addini ya yi rauni, to an kyale shi ne, amma in aka fara taba shi karfi yake yi. Kuma muna iya gani daga abinda suka mana abinda ake cewa, a yi ta manya-manya ta kare…”
A nan ne Jagora (H) ya yi bitan marhalolin da azzaluman mahukuntan kasar nan suka rika bi wajen afkawa ‘yan uwa, har zuwa lokacin da Zanqalele ya yi umurnin a yi ta manya-manya ta kare, ta hanyar bude wuta a kashe kowa, ciki har da mata da jarirai. Yace: “Da aka yi ta manya-manyan, ta kare? Wa ta kare masa? Kun ga wanda ya yi manya-manya ta karen, ta kare masa. Ba mulkin, ba ran. Saura kuma kowanne ka ganshi ya lalace, wani ka ganshi kamar kadangare, wani kamar jemage, gasu nan ba ko kyan gani.”
Da yake magana da iyalan Shahidai masu girma, Jagora Shaikh Zakzaky (H) ya ja hankalinsu akan kara hakuri da juriya a tafarkin Allah Ta’ala. Yace: “A kara hakuri, ai ta hakuri, ai ta hakuri, hakurin nan shi ne ke kambama lada.”
Jagora ya kara da cewa: “Mun san da daci. Idan ba daci, zai zama ba lada mai yawa. Tabbas da daci rabuwa da masoyi, saboda haka, dacin nan lada ne. Lokacin da har aka tuna aka yi hawaye, to lada ake samu. Saboda haka za mu rika tuna su. A lokaci guda, za mu ji dacin rabuwa da su, har mu yi hawaye, sannan kuma a lokaci guda mu ce, Masha Allah, Alhamdulillah, ba asara suka yi ba… Fatanmu shi ne, Allah Ta’ala, mu ma ya yi mana kyakkyawar karshe.”
Hari la yau, Jagora ya yi magana da masu aukar da Shahada ta hanyar kashe ma’abota addini da cewa: “Mun san ko mun muku magana ba za ku ji ba, amma kuna da hakkin mu yi muku wa’azi, don mu fita hakkinku. Sai mu ce da ku, don ku sani, ba za ku taba cin riba ba. Abinda kawai za ku iya yi shi ne, za ku yi kisan kai, za ku yi barna, amma abinda kuke so ku hana, ba zai hanu ta wannan hanyar ba. Habaka ma zai yi ta yi har ya tabbata. Kuma ku hasara za ku yi, a nan duniya da kuma a lahira. Wannan tabbas haka ne.”
Hari la yau, ya yi nasiha ga malaman fada, da kan baiwa Gwamnati fatawar ta kashe ma’abota addini da sunan ba komai. Yace: “Sai mu ce musu, ku ma ba za ku yi riba ba. Ku ba da kokari, kun san karya kuke yi, wallahi ba addini kuke yi ba. Kuna rudan kanku ne kawai.”
Harwayau, Jagora ya ja hankalin sauran al’umma ‘yan zura ido su ga waye zai yi nasara tsakanin ma’abota addini, da azzaluman da ke fada da su. Yace: “Za mu ce muku, ku zura ido din, amma wani abu guda; alkawarin Allah ne addini fa zai dawo. Kuma muna ganin alamomin da muke gani a duniya yanzu.”
Jagora (H) ya bayyana cewa, ba makawa sai an yi wannan gwabzawan da makiya Allah nan kusa. Yace: “Kun ga (kafircin duniya) suna ta barazana, ta kowane hali sun ce sai sun kai ma Iran hari. Yau Iran shekara 47 da juyin Musulunci, har yanzu basu kyale ta ba, ko yanzu ma barazanar za su kawo mata hari ta kowane hali ne, su kawo wannan dalilin, in ya kwaranye su sake kunno wani.” Yace: “To amma karshe gwabzawan nan za a yi na sosai din ne, kuma karshe ne lokacin da Imam (AJ) zai bayyana, kuma addinin nan sai ya mallaki duniyar nan gabadayanta. Wannan alkawarin Allah ne, kuma lallai wannan zai auku.”

Post a Comment