Ƙungiyar Cigaban Ilimi ta Garin Bomo Ta Gudanar da Taron Shekara-shekara (BEDA)


Ƙungiyar Cigaban Ilimi ta Garin Bomo, wato Bomo Education Development Association (BEDA), ta gudanar da taron ta na shekara-shekara a ranar 25 ga Janairu, 2026, a ɗakin taro na NAERLS da ke cikin Jami’ar Ahmadu Bello University (ABU), Zaria.

Alhaji Lawal Jibril Bomo ne ya jagoranci taron.

A yayin taron, an gabatar da jawaban ilmantarwa daban-daban. Daga cikin manyan baƙin da suka halarci taron akwai Farfesa Abdullahi Macido Bomo, Dr. Haruna Muhammad Jumare Bomo, Farfesa Abubakar Muhammad Jumare Bomo, Engr. Dr. Sani Yakubu Khalifa Bomo, Dr. Murjanatu Yusuf Usman Bomo, Dr. Abdulazeez Ibrahim, Barrista Ashiru Badamasi Bomo, Alhaji Mukhtar Salihu Sarkin Bomo, da Shugaban Karamar Hukumar Sabon Gari, Malam Jamilu Albany Samaru.

Bayan kammala taron, an karrama wasu daga cikin hazakakkun ɗaliban da suka kammala karatunsu a jami’o’i, inda aka miƙa musu kyaututtuka domin ƙarfafa musu gwiwa.

Limamin Masallacin Juma’a na Garin Bomo, Alhaji Tukur Dahur, ne ya rufe taron da addu’a.

Post a Comment

Previous Post Next Post