Nisf Sha’aban: Harisawa Sun Yi Aikin Gayya a Bauchi Unit

 


Daga Hurras Media

A cikin raya munasabar Nisf Sha’aban, ranar Juma’a 11 ga Sha’aban 1447H, Harisawan Bauchi Unit da ke ƙarƙashin Amiril Muminin (AS) Zone sun gudanar da aikin gayya domin tallafa wa al’umma, inda suka gina banɗaki da sashin wanka a gidan wasu marayu da Allah Ya yi wa mahaifinsu rasuwa.
Rahotanni sun nuna cewa katangar banɗakin da sashin wankan gidan sun rushe tun shekaru da dama da suka gabata, lamarin da ke jefa iyalan gidan cikin matsanancin hali. 
Harisawan sun haɗa kai tare da sadaukar da kuɗaɗensu, kayayyakin gini da lokacinsu domin kammala aikin cikin nasara.

Iyalan gidan sun nuna matuƙar farin ciki da jin daɗi bisa wannan taimako da aka yi musu, inda suka miƙa godiya ga Harisawan, tare da yi wa Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) addu’a bisa turbar tarbiyya da koyarwar da yake ɗora almajiransa a kai.

Baya ga hakan, Harisawan sun kuma kwashe dattin da ya toshe magudanar ruwa da ke kwance a lungunan injin niƙa a unguwar Kafofin Mafarki. 

An bayyana cewa magudanar ruwan na tara datti tsawon lokaci, lamarin da ke haddasa ambaliyar ruwa da barazana ga lafiyar mazauna yankin.

Ayyukan gayyar na daga cikin shirye-shiryen Harisawa na raya Nisf Sha’aban, tare da nufin ƙarfafa taimakon juna, tsaftar muhalli da kuma bunƙasa jin ƙai a cikin al’umma.

Post a Comment

Previous Post Next Post