Taron ƙara wa juna sani na ƙasa da ‘Youths Medical Care Initiatives’ ƙarƙashin jagorancin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ke gudanarwa, ya gudana a garin Kaduna.
Taron, wanda aka shiga rana ta biyu a ranar Asabar 27/12/2025, ya gudana ne a unguwar Nassarawa, Kaduna. An fara taron ne da addu’a, daga nan aka wuce kai tsaye zuwa ga jawabin farko daga bakin Dr. Najeeb Mai Gatari (MBBS), wanda ya yi bayani kan maudu’in:
“Rampant Cases of Kidney Problems in Nigeria: Causes and Proper Way Out”
wato “Yawaitar Cutar Ƙoda a Nijeriya: Dalilai da Hanyoyin Magance ta Cikakke.”
Bayan wannan ne Dr. Karima Saleh (MBBS) ta gabatar da maƙala kan maudu’in:
“Antimicrobial Resistance: Addressing the Growing Concern and Promoting Responsible National Antibiotic Use”
inda ta yi bayani kan matsalar tsananin juriya ga magungunan rigakafi da kuma hanyoyin amfani da su cikin natsuwa.
Daga bisani kuma, Dr. Zainab ta jagoranci bayani kan maudu’in:
“Emergency Obstetric and Newborn Care: Best Practices and Challenges,”
wato “Kula da mace mai juna biyu da jariri a lokutan gaggawa: Hanyoyin Aiki da Kalubale.”
Taron ya gudana tare da halartar masana da matasa daga sassa daban-daban na ƙasar.

Post a Comment