An kammala taron ranar Masoya Manzon Rahama (S) a garin Kaduna wanda aka mai take da Yaumur Rasul a ranar Lahadi 28 ga watan Disamba na shekarar 2025 (M) kamar yadda sanarwa ta gabata za a gudanar.
Taron de wanda shi ne karo na farko da al’ummar musulmi suka shirya waɗanda suka haɗa da yan Ɗarikarul Tijjaniya, Ƙadiriyya da almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky.
Kafin taron an soma da ɓudewa da addu’a da jawabin maraba da baƙi sannan karatun Alkur’ani, inda aka gabatar da Ɗaliban makarantu domin nuna soyayyar su ga Ma’aikin Allah .
Taron ya sama halartar mutane maza da mata manya da ƙanana da Shehunai da malamai da masana gami da yan siyasa domin nuna ƙauna ga Manzon Allah, wanda malamai da dama suka gudanar da jawabai daban-daban a muhallin taron wanda ya gudana a tsakiyan Tudun Wada kusa da Masallacin Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi.
An soma taron Lafiya an kammala Lafiya ga wasu Hotuna daga Wakilan mu.

Post a Comment