Daga Idishia Jos
Da yammacin jiya Lahadi 28 ga watan Disamba, 2025 Dandalin ‘yan’uwa mata Musulmi Almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) na Yankin Jos, suka gabatar da mauludin Ƴan Manzon Allah (Saww) Sayyida Zahra (S.A) a Markaz Anguwan Rogo Hussainiyyatu Sheikh Zakzaky (H).
Bayan bude taron da addu’a tare da gabatar da karatun Alkur’ani Mai Girma, an gabatar da waƙen yabo ga Sayyida Zahra (S.A) wanda Sha’irai harka Islamiyya suka yi a wajen. Yayin taron an Gabatar da Faretin girmamawa ga ƴar Manzon Allah (S) Sayyida Zahra wanda Ɗaliban Fudiyyah Jos suka yi a wajen.
An gabatar da Jabawai daga Manyan baki da suka samu halarta, babban bako da yayi jawabin kammalawa shine Dr. Sabi’u Adam Keffi wakilin ƴan uwa Musulmai Almajiran Sheikh Zakzaky (H) na garin Keffi. Yayi dogon jawabi akan samuwar Sayyida Zahra (S.A), yadda tazo duniya da kuma irin soyayya da kauna da Allah da Manzonsa suka mata.
Ƴan uwa Musulmai Almajiran Sheikh Zakzaky (H) na cikin garin Jos da wajen garin Jos, suka samu halarta Wannan taron mai albarka. Sannan an samu halarta wanda ba ƴan uwa ba (Amawa) daga mutanen gari da kuma wasu daga sashin ƴan uwa ƴan Ɗariku na Jos duka sun halarci wannan Mauludi da aka yi a jiya Lahadi.
Bayan kammala jawabinsa an yanka ‘Cake’ Sannan aka yi addu’a kammalawa. Wanda Malama Hauwa Rikkos ta jagoranta.

Post a Comment