Pakistan: Muna goyon bayan Tehran da yarjejeniyar JCPOA


Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Pakistan Tahir Hussain Andarabi, ya bayyana cewa Pakistan tana goyon bayan Iran da kuma yarjejeniyar yarjejeniyar nukiliya ta JCPOA. Hussain Andarabi ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai na mako-mako a birnin Islamabad, a matsayin martani ga matsayin da shugaban jamhuriyar Musulunci ta Iran Masoud Pezeshkian ya dauka, biyo bayan kalaman barazana da shugaban kasar Amurka da firaministan gwamnatin sahyoniyawan suka yi na cewa matsayin Pakistan kan batutuwan da suka shafi Iran da yarjeneiyar  JCPOA suna goyon bayan Iran ne kai tsaye. 

Ya kara da cewa a duk lokacin da Isra’ila ta kai hari kan Iran, Pakistan za ta goyi bayan Jamhuriyar Musulunci ta Iran. Da yake tsokaci kan bututun yarjejeniyar iskar gas tsakanin Iran da Pakistan, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Pakistan ya jaddada cewa Islamabad na ci gaba da jajircewa kan aikin ba tare da wani shayi ba.

Post a Comment

Previous Post Next Post