Daga Zainab Rauf, Abuja
Gidauniyar Zahra Relief Foundation ta bayyana cikakken shirinta na yin hadin gwiwa da Hukumar Kula da Ba da Jini ta Kasa (NBSA) domin karfafa al’adar ba da jini, bada agajin gaggawa, da kuma fadakar da al’umma, da nufin ceto rayuka a fadin Nijeriya.
An bayyana wannan kuduri ne yayin wata ziyarar bayar da shawarwari da Gidauniyar ta kai hedikwatar NBSA da ke Abuja a ranar Alhamis, 21 ga Janairu, 2026.
Da yake jawabi a yayin ziyarar, Shugaban Zahra Relief Foundation, Dakta Ibraheem Aqil, ya ce manufar jin kai ta Gidauniyar ta yi daidai da ta Hukumar Kula da Ba da Jini ta Kasa, musamman a bangarorin lafiya da taimakon gaggawa. Ya gode wa Darakta-Janar na Hukumar, Farfesa Saleh Yuguda, da shugabannin Hukumar bisa tarba da damar ganawa.
Dakta Aqil ya bayyana cewa Zahra Relief Foundation, wadda aka kafa a shekarar 2010 ta hannun jagoran Harkar Musulunci, Shaikh Ibraheem Zakzaky, gidauniya ce ta jin kai da aka yi wa rajista bisa doka, wadda ke da burin tallafa wa marasa karfi da mabukata a cikin al’umma. Ya ce Gidauniyar na gudanar da ayyuka a fannoni da dama, ciki har da kula da lafiya, taimakon gaggawa, ilimi, bunkasa al’umma, kula da marayu, da koyar da sana’o’in dogaro da kai.
A cewarsa, ayyukan Gidauniyar ba su takaita ga wani addini ko kabila ba, domin tana tallafa wa dukkan ‘yan Nijeriya ba tare da la’akari da addini, kabila ko matsayin zamantakewa ba.
Yayin da yake bayyana yiwuwar hadin gwiwa, Dakta Aqil ya ce Gidauniyar, ta hanyar Harkar Musulunci, tana da goyon baya a lungu da sakon kasar nan na dukkan jihohi 36 na tarayya da kuma Babban Birnin Tarayya. Ya ce ana iya amfani da wannan tasiri wajen shirya gangamin ba da jini a fadin kasar, kamar yadda aka taba yi a lokuta da dama a baya.
Ya kuma nuna cewa Gidauniyar kofar ta a bude take ga duk wani hadin gwiwa da Hukumar NBSA, musamman a fannoni kamar wayar da kan jama’a kan muhimmancin ba da jini, taimakon gaggawa, da shirye-shiryen kara samun kwarewa kamar horaswa da tarurruka, domin amfanin al’umma gaba daya.
A nasa jawabin, Darakta-Janar na Hukumar Kula da Ba da Jini ta Kasa, Farfesa Saleh Yuguda, ya yaba da ziyarar tare da jinjinawa Zahra Relief Foundation da mabiya Harkar Musulunci bisa dadaddiyar al’adarsu ta ba da jini kyauta, wanda ya ce hakan na taka muhimmiyar rawa wajen tallafa wa ayyukan Hukumar.
Farfesa Yuguda ya jaddada bukatar ganin ba da jini ya zama abu na dindindin ba tare da takaita shi ga lokacin Al-Muharram na shekara-shekara ba, yana mai cewa samun gudunmawar jini a duk tsawon shekara zai taimaka matuka wajen magance karancin jini da ake fuskanta akai-akai a kasar. Haka kuma ya bukaci Gidauniyar da ta taimaka wajen fadakar da jama’a domin su fahimci muhimmancin ba da jini a matsayin aikin ceto rayuka.
Daga bangaren Hukumar, manyan jami’an da suka halarci taron sun hada da Daraktan lura da hukumar, Daraktan Ayyukan Ba da Jini, da Daraktan Kudi da Lissafi. Tawagar Zahra Relief Foundation kuma ta kunshi Daraktan Lafiya, Daraktan Gudanar da Ayyuka, wakilin lura da gidauniyar, da sauran manyan jami’ai.
Ziyarar bayar da shawarwarin ta kara tabbatar da kudurin bangarorin biyu na karfafa hadin gwiwa domin inganta tsarin samar da jini a Nijeriya da kuma habaka sakamakon ayyukan lafiyar gaggawa a fadin kasa.

Post a Comment