Assalamu Alaikum Wa Rahmatulla.
Zahra Relief Foundation na sanar da al'umma shirin fara aikin ciyarwa na watan Ramadan mai alfarma na wannan shekara.
A shekarar da ta gabata, da tallafinku, an ciyar da mutane 3,735 abincin buɗa baki ga mabuƙata a wurare daban-daban.
A wannan karon, muna fatar ninka wannan adadin zuwa mutum dubu 12,000 in sha Allah, domin sauƙaƙawa ga mabuƙata kamar yadda Manzo (S) ya kwaɗaitar a huɗubarsa ta gaf da shiga Ramadan da cewa, "ku kiyaye kan ku daga wuta ko da da ɓarin dabino ne..." Ku yi sadaka ga mabuƙata da talakawa a cikin ku".
Muna kira ga al'umma da su anfana da É—inbin falala da lada da Allah Ya tanada a cikin ciyarwa a wannan wata mai alfarma.
Ana iya bayar da tallafi ta hanyar kuÉ—i, kayan abinci ko duk wani abu da zai taimaka wurin wannan aiki na ciyarwa.
Account: Zahra Relief Foundation Ramadan Feeding
Number: 1229615798
Zenith Bank
Allah Ya bada ikon tallafawa, Ya karɓa, Ya sanya a ma'auni, ilahi. Ramadan Mubarak.
Corporate Communications Department,
Zahra Relief Foundation

Post a Comment