Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai, salati da taslimi ga Shugaba, zaɓaɓɓe a cikin dukkan halittun Allah, kuma mafi soyuwar bayi a wajen Ubangiji Annabi Muhammad (SAWW) da Iyalansa zaɓaɓɓu, tsarkaka.
GABATARWA
Kafin shiga Ƙarni na Ashirin da ɗaya, bisa lissafin turawan yammacin duniya, sun tsara za su karkatar da hankulansu a kan sake mamaye nahiyar Afrika a karo na biyu. Ƙaruwar ilimi da hanyoyin bincike a ƙarni na ashirin ya sanya fahimtar da suke da shi akan ma’adinai da tasirin da nahiyar take da shi ta ƙaru har suka iya hango za ta iya jagorantar duniya a fannoni da dama, a ƙarnin da za a shiga. Hakan ya sanya suka fara shirin yadda za su sake mamaye ta don ya zama ba ta kufce musu ba, har ya zama al’ummar ta ta ƴantu, ta iya amfanuwa da arziƙin da ke a ƙasashen da suke. Wannan yana nufin idan ba su daƙile al’ummar ba, damarmakin na iya ɗora su a jagoranci na duniya, yiwuwar hakan a ganinsu na nufin rushewar iko da tinƙahonsu.
Nahiyar da a dunƙule take da sama da kaso 30 cikin 100 na arziƙin duniya gabaɗaya, ta ke jagoranci da kaso mafi tsoka (2/3) a Ma’adinai da su ne ginshiƙai a ci gaba da ƙere-ƙeren fasaha (Emerging technology) a ƙarni na ashirin da ɗaya. Nahiyar da ta ke da matashiyar al’umma wadda kusan kaso 60-70 na ta ya ƙunshi matasa masu shekaru 40 zuwa ƙasa, take da al’ummar dake ƙaruwa wato (Growing population) take da kyawawan al’adu da tarihi mai muhimmanci, idan har ba a dakatar da ita ba, za ta kai ga cimma wannan hasashe.
Saboda haka daga ƙarshen ƙarni na ashirin bayan rushewar daular Soviet zuwa farkon sabon ƙarni sai hankali ya fara karkata zuwa ga Afrika. Ƙasashen Yammaci da gabashin duniya su kai dirar mikiya wajen cimma hadafofin su a yankin; Amurka da tsare-tsarenta na Millennium Challenge Acoount (MCA) da Free Trade Agreements (FTA), Ƙasashen Turai kuma suka sake zuwa da sabbin yarjejeniyoyi da za su ci gaba da kame ƙasashen da suke yiwa Mulkin Mallaka. Russia, China da sauran gabashi su ma da nasu tsarurrukan yarjeniyoyin na mu’amalar tattalin arzikin, musamman dabarun matse maƙogaron ƙasashe da basussuka don samun gindin zama a nahiyar.
Sai dai ba a kai shekara 5 a cikin sabon ƙarnin, Amurka da ƙawayenta suka fara canja lissafin su na danniya a faɗin duniya cikin fasalin jefa yaƙe-yaƙe da sunan yaƙi da ta’addanci. A kai tsaye suka lissafa wasu yankuna a Afrika cikin lissafin wuraren da za su yaƙa, duk da babu wani dalili na kai tsaye a bayyane ko kuma hujja da za su yi amfani da ita a lokacin da zai sa su ambata haka. A yanzu mun ci kashi ɗaya bisa huɗu na ƙarnin, kusan dukkan yankunan Afrika sun rikice, yaƙe-yaƙe suna ta ƙaruwa ta kowacce kusurwa, gwamnatoci na wargajewa, tattalin arziƙi na cigaba da durƙushewa, alƙiblar yankin na canjawa daga ƙyakkyawan fata da cigaba zuwa wani yanayi mai ban tsoro.
Abun da zamu duba a wannan takarda shi ne ta yaya zamu fahimci alƙiblar da aka ɗora nahiyarmu a kai cikin shekaru 25 da suka gabata, wane irin salo na mamaya mu ke fuskanta a yanzu? irin na farko ne ko wanda ya fi shi muni? Sannan a wane yanayi ne zamu iya gina aikin da zai ceto wannan al’umma daga bala’in da aka jefa ta a ciki har ya zama mun juyar da aikin ƴan mamaya zuwa ga nasarar wannan al’umma.
ƊABI’AR TINƘAHO DA DANNIYA NA ƳAN MAMAYA
Tarihi ya karantar da ɗabi’ar tinƙaho da danniya da ƴan mamaya a wannan zamani suke da su a matsayin cututtuka da suke kama masu ƙarfin iko da suka rasa kyawawan ɗabi’u tattare da su waɗanda ɗan adamtaka ta ginu akan su, waɗannan ɗabi’u basu keɓanta ga wani jinsi ba, sai dai tasirin ƙarfin iko ga masu riƙe da dauloli idan sun rasa tarbiyya ta kyawawan ɗabi’u.
Amma duk da wannan tinƙahon da son danniya da kwaɗayin su ga arziƙin da masu rauni suke da shi, wayon ɗan adam a cikin siyasa da gudanar da mulkin al’umma ya koya musu bin hanyoyin makirci da dabaru a haɗe da sanya ƙarfi wajen ganin sun samu iko da tasarrufi da dukiyoyin al’ummomin da su ke dannewa ko suke shirin dannewa.
Wani masanin Falsafar al’ummar Afrika ya kalli dabarar rusa al’umma, shugabantar da lalatattun cikin su da dabarar faɗaɗa matsalolin tarihi da ke cikin al’umma don samun damar rarraba su a matsayin dabarun da ƴan mamaya sukai amfani wajen samun iko akan al’ummun Afrika a mamaya ta farko. Shi kuwa Julius Nyerere ƙarawa ya yi da cewa: Kamar yadda Turawa sukai amfani da bambance- bambance na ƙabilu wajen samun damar rarraba al’ummar Afrika, rusa ta da mulkar ta, idan har za su sake mamaye ta a gaba za ku ga sun ɓullo da dabarun tarwatsa ƙasashe (da suka kafa), karkasa su zuwa ƙanana da jefa rikice-rikice a cikin su yadda rauni zai yawaita a tsakanin su, sai su cimma muradan su cikin sauki.
RUSA AL’UMMA: BABBAN MAKAMIN MAMAYA
Kyakkyawan tunani ga al’umma shi ne sinadarin ci gaban kowacce al’umma, wanda yake samuwa a cikin tarbiyyar ilimi, tarihi da al’adun ta. Fiƙrar da al’umma ta ginu akan ta, akan ta imanin ta da kishinta su ke ɗoruwa. A duk lokacin da tarbiyyar Ilimi ta al’umma ta munana, fahimtar al’ummar ga haƙiƙanin tarihin ta ya ƙaranta sannan rugujewar al’adu kyawawa da gina munana ya yawaita, lallai wannan al’ummar na fuskantar rushewa.
Waɗannan matakan na rusa al’umma duka Turawan Mulkin mallaka a mamayar su ta farko sun yi amfani dasu wajen rusa wannan nahiyar da canja mata alƙibla daga al’umma mai alfahari da ci gaba zuwa cibayayyiya da ta zamo mai rauni abar juyawa.
A ƙarni na ashirin da ɗaya cikin shekaru 25 mun ga nunnunkuwar lalacewa a waɗannan ɓangarori ta hanyar ayyuka daban-daban da suka yawaita a wannan nahiyar. Matashiyar al’ummar da Afrika take da ita ta zama cibayayyiya a tarbiyyar Ilimi, wadda ba ta san tarihinta ba, kuma aka mantar da ita cutarwar da Turawan yammaci suka yiwa nahiyar a mulkin mallaka har ya zama da yawa suna musu kallon masoya kuma abokai, a lokaci guda muna ganin yadda ake tafka maƙudan kuɗaɗe wajen kashe al’ummar da abubuwan da za su lalata musu lafiyar gangar jiki da gusar musu da hankali.
Lallai duk al’ummar da take tafiya a wannan tsari kai tsaye tana tafiya zuwa maƙabartar tarihi ne, ko kuma ramukan da ƴan mamaya suka tanadar mata na dauwamammiyar bauta. Al’ummar da aka yi nasarar rusa ta ana fara mamaye tunanin ta kafin bayyanar sojoji a iyakokinta, alamar hakan na iya bayyana a cikin ɗabi’un ko-in-kula akan makomar ta daga matasan ta, da bayyanar rashin soyayyar ta a zukatan su, ballantana a samu ayyukan sadaukarwa a tattare dasu gare ta.
GINA AL’UMMA MAI AZAMA DA ƘUMAJI: AIKIN DAKE GABAN MU WAJEN CETON AL’UMMA
A wannan lokaci da aka shiga kashi na biyu bisa huɗu na ƙarni na ashirin da ɗaya, a nahiyar Afrika da ayyukan ƴan mamaya su ke sake bayyana, musamman yammacin Afrika, halin da ake ciki da makomar wannan al’umma tana sake fitowa fili ga kowa. Kashe-kashe da sunan addini da ƙabila, durkushewar tattalin arziki, kwashe haziƙan matasan al’umma zuwa ga ƙasashen yamma yana nuni da mummunar gobe a wannan al’umma.
Aikin gina al’umma ta fuskacin tunani, tarbiyyantar da su da raya zukatansu shi zai samar musu da ƙumaji da fiƙra shi zai shirya su a aikin da yake gabatowa wanda aiki ne na dukkan al’umma gabaɗaya. Samar da al’ummar da take tare da sahihin tarihinta, kuma take da zuzzurfan fahimta akan addininta da al’adu masu rayar da zukatan ta shi zai sanya dawowar fata, domin da haka ne al’ummar za ta iya tunƙarar dukkan abunda masu tinƙaho za su zo dashi, kuma ta yi nasara.
Amma wannan aiki ba zai taɓa zama mai sauƙi ba, koda akwai masu burin aikata shi idan basu shiryawa abun da ya dace da aikin ba. Mu sani manyan matsalolin aikin ba za a lissafa su akan yunƙurin kisa ko kawar da masu ƙoƙarin kawo gyara ba, sai dai a cikin irin shirin da ake da buƙatar masu aikin su yiwa kan su na ilimi, sadaukarwa, jajircewa da kyakkyawan tarbiyya na ruhi da za su sa su iya tsayuwa a gaban aiki da shirin Azzalumai ƴan Mamaya.
An karanta a taron Mauludin Abulfadl Abbas (AS), 1447H/2026, Abuja, Nigeria.

Post a Comment