A ranar Juma’a 4 ga watan Sha’aban, 1447H daidai da 23 ga watan Janairu, 2026; Mu’assasatu Abul Fadl Abbas Ƙarƙashin Jagorancin Shaikh Ibraheem Ya’qoub Zakzaky (H) ta gudanar da maulidin Sayyid Abul Fadl Abbas, Imam Sajjad (A.S) tare da tunawa da gwarazan Shahidan Mu’assasatu Abul Fadl Abbas (A.S) a garin Abuja.
An fara taron da buɗewa da addu’a, karatun Alƙur’ani mai girma, tare da ziyara. Mawaƙa sun ƙayata muhallin taron da waƙoƙin maulidin da na gwarazan shahidai masu girma, Firqatu Shahid Humaid sun gabatar da Display.
Farfesa Hassan Isah Mshelgaru, ya gabatar da jawabi akan maudu’i mai taken: ‘Rashin Ninanci – Tushen Sadaukarwa, Darussa Daga Rayuwar Sayyid Abul Fadl Abbas (A.S)’.
Bayan Farfesa ya kammala Malam Ibrahim Abubakar Mamunu, ya gabatar da takarda mai taken; MAMAYAR AFRIKA KARO NA BIYU: nauyin da ya hau kan matasa, wajen ceto wannan al’umma.
Da wannan aka kawo ƙarshen Maulidin sai aka fara da tunawa da Shahidan Abul Fadl.
Malam Jamilu Bauchi, ya gabatar da takaitaccen jawabi akan Abbas Shuhada tare da jaddada alƙawari, bayan nan sai display/Ma’atam daga ajiyayyun waƙoƙin Mu’assasatu Abul Fadl Abbas wanda membobin Intizarul Imamul Muntazar suka gabatar.
A ƙarshe an miƙa abin jawabi ga Ummush Shuhada Malama Zinatuddeen Ibrahim, ta gudanar da jawabi akan shuhada, tare da yanka alkaki, sai aka biyo da jawabin godiya wanda Malam Mujaheed Ali, ya yi, Malam Sa’idu Birnin Kudu, ya rufe taron da addu’a.
Wasu takaitattun hotuna na yadda wannan taron ya gudana.
.jpg)
Post a Comment