Kotun ɗaukaka ƙara da ke garin Ilorin a jihar Kwara ta tabbatar da hukuncin kisa da aka yanke wa wasu mutane biyar da aka samu da laifin fashi da makami a wani banki a garin Offa a shekarar 2018. Daraktan sashen shigar da ƙara na jihar, Mohammed Akande, ya bayyana cewa duka alƙalai uku na kotun sun amince da hukuncin da babbar kotu ta yanke na kisa ta hanyar rataya.
Wani jami’in kotun ya kuma ce kotun ta yi watsi da duka hujjojin waɗanda aka yankewa hukuncin suka shigar kuma ta ba da umarnin a mayar da su gidan yari cikin gaggawa. Ko da yake waɗanda aka yanke wa hukuncin suna da ƴancin tunkarar kotun ƙoli, jami’in ya ce hujjojin da aka gabatar a kotun ɗaukaka kara ba su da gamsarwa kuma da wuya sau yi nasara ba idan aka maimaita su a kotun ƙoli.
Hukuncin dai ya samo asali ne daga wani fashin banki a watan Afrilun 2018 a ƙaramar hukumar Offa ta jihar Kwara, inda aka kai hari kan bankunan kasuwanci guda biyar. Aƙalla mutane 32 ne aka kashe, ciki har da ƴan sanda tara, biyu daga cikinsu mata ne, lamarin da ya sa ya kasance ɗaya daga cikin fashin banki mafi muni a tarihin Najeriya. .

Post a Comment