Tsauri Ba Rashin Ladabi Ba Ne a Aikin Jarida


Daga Ammar M. Rajab 

Ni ba 'fan' ɗin BBC Hausa ba ne. Hasalima, na daɗe da 'unfollowing' shafukansu. Abin da kawai ke sa in ga wasu daga cikin labaransu shi ne idan 'abokai' a Facebook suka yi 'sharing'. Duk da haka, hayaniyar da ta biyo bayan hirar da ƙwararriyar ‘yar jarida Madina Maishanu ta yi da Gwamnan Neja, Umar Bago, da Ministan Tsaro, CG Musa, da kuma Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ta tilasta min in yi tsokaci.

Abin da wannan muhawara ta bayyana shi ne cewa mutane da dama sun rikita aikin jarida na ƙwarai da aikin jarida na raha da nishaɗi. Sun saba da ‘yan jarida masu dariya, tumasanci da sassauta magana — har ta kai ga barin baƙi (waɗanda ake tattaunawa da su) su kauce wa tambayoyi masu muhimmanci. Duk wanda ya saba da irin wannan salo, tabbas zai ga tsaurin Madina a matsayin rashin ladabi. Amma a gaskiya, abin da ta yi shi ne ainihin aikin jarida.

Duk mai kallon shirin MAHANGAR ZAMANI na BBC Hausa ya san cewa Madina Maishanu na iya hira cikin annashuwa, fara’a da nishaɗi idan yanayin shirin ya buƙaci hakan. Domin shiri ne na zamantakewa da rayuwa. Amma ƙwarewa a aikin jarida ba wai iya raha kaɗai ba ce; ƙwarewa ita ce iya sauya salo gwargwadon batun da ake tattaunawa. 

Hirar da ta yi da Gwamna Bago, CG Musa da Sanata Kwankwaso ba hira ce ta nishaɗi ba. Hira ce kan tsaro, siyasa, rayuwar al’umma, da makomar ƙasa. Waɗannan batutuwa ba sa buƙatar dariya; suna buƙatar tsauri, tambayoyi kai-tsaye, da matsa lamba domin a amsa.

Bisa ƙa’idar aikin jarida, mai gabatar da hira na da cikakken ikon:

*katse baƙo idan ya kauce wa tambaya,

*dawo da shi kan batu idan ya fara zagaye-zagaye,

ko kuma taƙaita maganarsa saboda lokaci.

A talabijin da rediyo, lokaci abu ne mai tsada, ba a barin wanda ake tattaunawa da shi ya cika shi da bayanan da ba su da alaƙa da tambaya.

Saboda haka, abin da Madina Maishanu ta yi bai saɓa wa ƙa’idar aikin jarida ba. Abin da kawai ta saɓa wa shi ne abin da wasu suka saba gani. Matsalar ba a kan Madina take ba; matsalar tana kan masu kallo da suka ɗauki ɗan jarida a matsayin mai nishaɗantarwa, ba mai tambayar gaskiya da ƙwaƙƙwafi ba. 

A ƙa’ida, aikin ɗan jarida shi ne yin tambayar da ta dace. Aikin jami'i ko ɗan siyasa shi ne ya amsa — ko ya ƙi. Ba aikin ɗan jarida ba ne ta tausasa tambaya ko ta sauƙaƙa wa mai iko hanyar kauce wa gaskiya.

Idan har muna son aikin jarida mai amfani ga al’umma, dole ne mu daina hukunta ‘yan jarida saboda tsaurin su, mu fara hukunta rashin amsa tambayoyi da kauce ma gaskiya. Domin a ƙarshe, ‘yan jarida ba maƙiya ba ne; wakilan al'umma ne.


Post a Comment

Previous Post Next Post