Atiku Ya Bukaci Majalisar Dattawa Ta Gaggauta Gyara Dokar Zabe Don Hana Magudi A 2027


Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya bukaci majalisar dattawan Nijeriya da ta yi hanzarin sake dubawa da amincewa da gyara dokar zabe ta 2022, yana gargadin cewa gibin da ke cikin doka ya taimaka wajen samun rashin daidaito a lokacin zaben 2023. 

A cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Atiku ya bayyana cewa tsarin doka na yanzu ya sa ya zama ba zai yiwuwa ba ga masu daukar karar su gabatar da shari’o’insu a kotu,” wanda ya haifar da yanayi da ya bai wa abin da ya bayyana a matsayin babban magudi a shekarar 2023. “A lokacin da kurakuran zabukan shekarar 2023 kenan a fili, wajibi ne a sake duba dokokin da ake amfani da su wajen gudanar da zabukan 2027 da na gaba,” in ji Atiku. 

Ya nuna damuwa kan yadda majalisar dattawa ta kuduri aniyar jinkirta ko kawo cikas ga zartar da gyare-gyare, yana mai ambaton rahoton kwanan nan da Gidauniyar Aikin Jarida ta Bincike (FIJ) ta yi a matsayin tuhuma na rashin daukar mataki na majalisa. “Sahihin zabe a 2027 ya dogara ne kan gaggawar da majalisar dattawa za ta nuna wajen daukar mataki kan wannan muhimmin doka. Yana da matukar muhimmanci ga majalisar dattawa ta kammala gyare-gyaren dokar kuma ta tabbatar cewa sabon doka ce ke tsara yadda za a gudanar da zaben 2027. 

Rashin yi hakan, nana cewa akwai yunkurin yin magudi a jefa kuri’u,” in ji Atiku. “Babbar koma baya ga zaben 2023 ita ce, wagegen gibin da ke cikin dokar zabe ta 2022, wanda ya ba da damar yin magudi a bude a wannan zaben, da kuma rashin bai wa masu koke damar gabatar da shari’arsu a gaban kotu. “Yana da muhimmanci idan za a gyara kurakuran zaben shekarar 2023, ya kamata a sake duba dokokin don toshe hanyoyin magudi a zaben 2027 da mana gaba. “Amma a halin da ake ciki, a bayyane yake cewa majalisar dattawa ta kuduri aniyar kawo cikas ga gyare-gyaren dokar zabe ta 2022. “Rahoton da gidauniyar FIJ ta fitar kwanan nan yana matsayin zargin majalisar dattawa da kuma kiran gaggawa na sauke alhakin dokoki. Gudanar da sahihin zabe a 2027 yana dogara ne kan gaggawar da majalisar dattawa za ta nuna wajen magance wannan muhimmin kudiri. 

“Saboda haka, yana da muhimmanci majalisar dattawa ta kammala sauye-sauyen dokokin kuma ta tabbatar da cewa dokar ta zamani ce ke za ta kula da gudanar da zaben shekarar 2027. Kasa da wannan kokari na nufin tsara zabe tun kafin a jefa kuri’u.”

Post a Comment

Previous Post Next Post