Yadda ’Yan Uwa Musulmai Almajiran Sheikh Ibrahim Zakzaky (H) na Garin Dukke, Karamar Hukumar Funtua, Suka Gudanar da Aikin Gyaran Dukke Primary School’.
Yan uwa Musulmai Almajiran Sheikh Ibrahim Zakzaky (H) na garin Dukke, da ke Karamar Hukumar Funtua, sun gudanar da aikin gyaran harabar Dukke Primary School sakamakon lalacewar da makarantar ta samu saboda rashin hanyar wucewar ruwan da ke kwarara daga rijiyar burtsatse (borehole).
An gudanar da wannan aiki ne a yau, Asabar, 27 ga Disamba, 2025, domin gyara matsalolin da ke haddasa taruwar ruwa da lalata harabar makarantar, lamarin da ke kawo cikas ga koyarwa da koyo.’Yan uwantakar sun bayyana cewa aikin ya kasance wani bangare na gudummawar al’umma domin tallafa wa ilimi da inganta muhallin makarantu.
Muna fatan Allah Ya karɓi ayyuka da kyakkyawar niyyar ’yan uwa, Ya sanya su a mizani, Ya kuma saka musu da alheri.

Post a Comment