A ranar Alhamis, 25—12—2025, Dandalin Matasan Harkar Musulunci ƙarƙashin jagorancin Sayyid Ibraheem Yaqoub Zakzaky na garin Dandume, dake Sayyid Zakzaky Zone (Funtua), sun kai ziyarar taya murna ga kiristoci a cikin bukukuwan Kirismeti a garin Dandume. Da yake gabatar da jawabi a yayin ziyarar, Fasto Abubakar Musa, dake Cocin Catholic Church, ya bayyana jagora Sayyid Zakzaky (H) a matsayin mutum mai son zaman lafiya da hada kan al'umma baki ɗaya.
Fasto ya ƙara da cewa: “Mun gode da wannan ziyarar da kuka kawo mana, kunji dadi sosai. Allah ya karama dankon zumunci, Ubangiji Allah ya sanya maku albarka da wannan zumunci.” Shima Fasto Ayuba Musa, na Cocin ECWA, ya bayyana farin cikin sa matuka akan wannan ziyarar, inda yake cewa: “Yan Shi’a mutanen Alzakzaky kuna da zumunci da son jama’a ba tare da banbancin addini ba. Muna godiya gare ku sosai da wannan ziyara.”
Faston Cocin Assemblies of God, ya sanya ma ‘yan uwa albarka sosai da wannan ziyara, wanda yake cewa: “Dukanin mu yan Adam ne. Littafin mu mai tsarki ya nuna mana cewa ku taya masu farin ciki-farin ciki; haka kuma ku taya masu bakin ciki-bakin ciki. Muna jinjina maku sosai.” A lokacin ziyarar, an rika karanta sakon Kirsimeti na Dandalin Matasa tare da basu kofi na takardar.

Post a Comment