Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un. Jihar Bauchi ta yi babban rashi sakamakon rasuwar fitaccen ɗan jarida kuma gogaggen ma’aikacin kafar watsa labarai, Malam Dalhat Hamid Bello, wanda ya rasu a daren Asabar bayan fama da ‘yar gajeriyar rashin lafiya.
Rahotanni sun tabbatar da cewa Malam Dalhat ya rasu ne a Asibitin Koyarwa na Abubakar Tafawa Balewa (ATBUTH) da ke Bauchi, inda aka garzaya da shi domin karɓar kulawar likitoci. Marigayin ya shahara matuƙa a fagen aikin jarida, inda kafin rasuwarsa ya rike mukamin Shugaban Sashen Shirye-shirye na Gidan Rediyon Bauchi (BRC).
Haka kuma, ya taba rike matsayin Overseeing Managing Director na gidan rediyon kafin ya yi ritaya daga aikin gwamnati. Masu bibiyar harkokin watsa labarai sun bayyana Malam Dalhat a matsayin mutum mai jajircewa, gaskiya da ƙwarewa, wanda ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen bunƙasa aikin jarida da shirye-shiryen rediyo a Jihar Bauchi da ma ƙasa baki ɗaya. Tuni aka yi sallar jana’izarsa a ranar Lahadi da misalin ƙarfe 10:00 na safe, a gidansa da ke kan titin Railway, cikin garin Bauchi.
Allah Madaukakin Sarki Ya gafarta masa kurakuransa, Ya sanya Aljannar Firdausi ce makomarsa, Ya kuma ba iyalansa da al’ummar jarida haƙurin jure wannan babban rashi. Ameen.

Post a Comment