An Gudanar Da Gagarumin Maulidin Imam Ali Bin Abu Talib (AS) A Garin Bomo

Daga Mardiyya Kabiru

A ranar Lahadi 09/02/2025 dandalin matasa almajiran Sayyid Ibrahim Zakzaky(h)na garin Bomo Suka Shirya Gagarumin Mauludin Iman Aliy Bin Abu Talib(A S). 

An fara da bude taro da addua sai Kuma karatun Qur'ani daga Mardiyya Sa'eed sai ziyarar iman Aliy wacce Mardiyya saleh ta karanta 

Ittahadu shu'ara suma sun nuna nasu soyyayar ga shugaban mumunai Iman Aliy (A S) ta hanyar wake shi da sukayi da gwalagwalan baitoci 

Manzon Allah(s)yana cewa inama anta munzirun walikulli qaumin hadd (Lallai ni mai wa'azantar wane kuma kowace Al'ummar tanada mai shiryatar da ita Inda manzon Allah yake nuni da Cewa iman Aliy mai shiryatarwa_____duk acikin darajojin iman Aliy Wanda Alhassan Yahya ya jagoranta kawoshi 

Sai jawabi daga bakin malama Hafsat jushi wacce Kadija Abdullahi ta gabatar da ita 

Daga cikin jawabin malamar ______

Bayan manzon Allah babu Wanda yakai iman Aliy ilmi saboda yasha ilmin ne awajen manzon Allah(S)inda ya zama manzon Allah ne gidan ilmi Aliy ne kofar shigarta 

Addini bai tsaya da kafarsa ba face da tsayuwar iman Aliy dan Abu Talib inda ya zama jarumin da babu kamarsa ta yadda yazama garkuwa ga addinin musulunci gaba daya 

Iman Aliy shine ya zama jarumin daya fanshi ran manzon Allah(s) lokacin da mutanen makka suka shirya su kashe manzon Allah inda ya yarda ya kwanta akan gadon manzon Allah(s) adaren hijra 

Da Itace da duwatsu zasu zama abin rubutu  to sunyi kadan su rubuta yawan darajojin da iman Aliy yake dashi 

Idan kanaso kaga Al'qurani a aikace to kayi duba zuwa ga Aliyu Dan Abu Talib_______kadan daga cikin jawabin da malamar ta gabatar kenan a wajen program 

Sai yanke Alkaki Wanda malam Aliyu Dahiru ya jagoranta  

Sai rufe taro da addua wacce babbar malamar ta rufe taron. 

Post a Comment

Previous Post Next Post