Daga ciki tace Babu gudu Babu ja da baya Babu bada hakuri ga Nuhu Ribado wannan jawaban nata martani ne da Barazana da take fuskanta ga Nuhu Ribado ta hanyar amfani da karnukan farautarsa da Kuma lauyarsa Ahmad Raji.
Biyo bayan kalaman nata dake cewa shugaban hukumar EFCC a wancan lokacin Nuhu Ribado ya fito bainan jama'a ya kwatanta gwamnar jahar Lagos a wancan lokacin Bola Ahmad Tunubu a cewa kasurgumin dan rashawa ma'aikacin gwamnati Wanda Bai isa ya guje ma shara'a ba.
Duk da cewa Nuhu Ribado ya mance da wannan kalaman ko Kuma ya zaba ya janye kalaman nasa na baya Ina tsaye kan gaba da kalamai na Kuma ban amince da cewa akwai bukatar neman gafaransa ba.
Daga ciki tana cewa wa zata baiwa hakuri shugaba tunubu da Mai bashi shawara akan harkokin tsaro a yanzu ya zargeshi da cin hanci a baya ko Kuma Nuhu Ribado da ya zaba Yace ya manta kalaman nasa.
Shugaban kungiyar tace bazata taba janye kalaman nata ba Kuma bazata bada hakuri ba kalmomin nata daidai suke da fahimtar ta kan wannan dambarwa duba da la'akari da abinda ke faruwa a kasar nan Kuma ban yadda cewa akwai bukatar neman gafaransa ba.
Naja'atu ta Kara da cewa bazata taba wasa da kimartaba wajen farantawa Wani ba da karnukan farautarsa ba
Tana Kara jaddada cewa bazata janye wannan kalaman ba ko neman gafaransa don kawai ta baiyana gaskiya a yadda ta ganta.
Ta Kara da cewa kamar yadda Nuhu Ribado yayi mata barazana wajen kaita kotu to ya gaggauta yin haka Kuma bazai rufe mata Baki ba, Kuma Babu Wanda zai zare mata ido saboda tana rayuwa ne don mutane masu kima ba irinsu ba.
Sannan ta baiyana cewa cikin sa'oi 48 ta fuskanci barazana kala kala da Kuma kiraye kiraye dake baiyana cewa Nuhu Ribado ya aiko karnukan farautarsa dasu kamata sannan abin kunyane su karnukan farautarsa sun sanar da ita kafin suzo wannan dalilin ne yasa ake cin zarafin 'yan gwagwarmaya masu fadar gaskiya.
A Karke shugaban kungiyar matasa wato NORTHERN STARS na cewa ta samu gamsassun bayanai cewa ana Shirin amfani da bangaren shara'a domin tilastani na janye wannan kalaman sannan na baiyana cewa Nuhu Ribado yayi abin kunya sannan ya janyoma shugaban nasa abin kunya Kuma Bai isa yayi mata barazana ba wajen fadin gaskiya ba a yadda ta fahimceta .
Sanna ta baiyana cewa Babu Wani adadin barazana da za'ayi mata Babu Wani gidan yari da take tsoro a duniya gidan yarin da take tsoro shine kawai kabari, Sannan tace ko kabarin Bata tsoransa saboda tanada kyakkyawan alaqa da mahaliccinta.
Sannan tace Nuhu Ribado yayi abinda yakeso ita kam tana tsaye kan kalaman nata.
Post a Comment